Wasu kwamandojin Boko Haram biyu, Ibrahim Muhammed da Auwal Muhammed, sun mika wuya ga sojojin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF da ke Monguno a Jihar Borno.
Rundunar MNJTF ta hada da kasashe da dama da suka hada da rundunar sojin kasashe irin su Benin, Kamaru, Chadi, Nijar da muma Nijeriya.
- Tarihi Da Darussa 7 Daga Yaƙin Badar Da Aka Gwabza Ranar 17, Ga Ramadan
- Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Samar Da Daidaitaccen Tunanin Raya Kasa
Rundunar tana da hedikwata a N’Djamena, babban birnin kasar Chadi kuma tana yaki da ta’addancin Boko Haram.
Shugaban yada labaran rundunar, Lafkanar Kanal Abubakar Abdullahi ne, ya bayyana a ranar Talata, inda ya bayyana cewa Kwamandojin biyu sun mika wuya ne bayan sun shafe fiye da shekara 10 suna aikata ta’addanci.
Abdullahi ya kuma bayyana cewa, a yayin bincike, maharan biyu sun amince za su taimaka wa rundunar da bayanai don samun nasarar dakile abokan aikinsu.
“An kwato makamai daga hannun ‘yan ta’addan da suka mika wuya.
“Kayan da aka kwato daga hannun Ibrahim Muhammed sun hada da bindigogi kirar AK-47 guda biyu, harsashin AK-47 guda uku da wayar hannu guda daya.
“Daga Auwal Mohammed, mun kwato kunshin harsashi guda biyar, wayar salula guda daya, gurneti biyu da sauransu,” in ji Abdullahi.