An yi wa mataimakin shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, tiyata a kafarsa a yau Asabar, bayan kwantar da shi da aka yi a asibiti.
Mataimakin shugaban kasar ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.
Sanarwa ta ci gaba da cewa mataimakin shugaban kasar ya ji raunin ne yayin wasan sukwas.
Nan gaba kadan likitocinsa za su yi bayanin halin da ake ciki dangane da aikin kafar tasa.