An fara kai ruwa rana tsakanin masu gidage da ‘yan haya a Nijeriya sakamakon matsin tattalin arziki.
An dai fara ki ruwa ranan ne saboda rashin samun damar biyan kudaden haya da mafi akasarin masu ‘yan haya ba sa yi sanadiyar halin kuncin rayuwar da ake fuskanta.
- Gwamnatin Nasarawa Ta Bukaci Shugaban ALGON Da Ya Daukaka Daarajar Jihar A Idon ‘Yan Nijeriya
- Kotu Ta Tsare Wani Mutum Kan Yi Wa ‘Yar Shekaru 11 Ciki A Legas
Binciken Jaridar LEADERSHIP ya gano cewa akwai irin wadannan matsalolin da suka sa har sai da lamarin ya kai ga kotu sanadiyar rashin biyan kudin haya kamar yadda aka saba biya.
Mazauna gidajen haya ba karamar matsala suke fuskanta ba sanadiyar rashin samun damar biyan kudaden haya kamar yadda aka saba biya, lamarin ya faru ne sakamakon koma-bayan da aka samu na rashin samun kudade a hannun ma’aikata da wadanda suke zaman kansu wanda ya je fa masu haya cikin tulin bashi.
Irin hakan ne ya sa masu gidajen suke zabar irin mutanen da za su zauna a gidajensu, wasu daga cikin suna bayar da hayan gidajen nasu tare da inshore.
Binciken ya nuna yawancin wadanda ake bin bashin kudaden haya su ne gaba-gaba wajen yin yin bukukuwa, zuwa wuraren cin abinci da wuraren holewa. Hakan ne ke sa yawancin masu gidajen ke daukar matakin kotu kan ‘yan hayansu.
Lamarin ya zo ne lokacin da ‘yan Nijeriya ke fuskantar babbar matsalar tattalin arziki da tsadar tafiyar da rayuwar yau da kullum da kuma hauhawar farashin kayayyakin abinci.
Tunanin samun dama ta biyan kuddin hayar abin sai kara darkushewa yake ga ‘yan hanayan da ake bi bashi, saboda farashin kayan gini ya yi tashin gwauron zabi wanda ya janyo kasuwanni da yawa suna rufewa, lamarin da ke sa masu karamin karfi suke rayuwar hannu-baka-hannu-kwarya.
Kamar dai yadda tsohon shugaban kungiyar masu gidajen haya na kasa (FIABCI), Mista Chudi Ubosi, ya ce ku san ana iya cewar kowane bangare lamarin ya shafi.
Ya ce gaskiyar lamarin ya shafi duk wasu harkokin rayuwa. Ubosi ya ce babu wani nuna bambanci a lamarin da ya shafi bayar da gidan haya, sai dai wasu masu bayar dagidajen hayan ne ke korar masu haya wadanda suka kasa cika alkawarin biyan kudi.
“A matsayinmu na kwararu ta bangaren bayar da gidaje haya ba ma mamakin kan abin ke faruwa a halin yanzu. A matsayinmu na wadanda suka mallaki gidajen haya wannn wani lokaci ne mai hatsari a garemu.”
Wani rahoton da ya shafi harkar gidaje a Nijeriya da kamfanin Pison Housing ya bayar a kan irin dambarwar da ake ciki na hayan gidaje, rahoton ya nuna cewa Nijeriya ita ce kasa ta daya da ke da masu zama gidan haya da suka kai kamar kashi 80.
Wani mazaunin Apapa da ke Jihar Legas, wanda baya son a bayyana sunansa ya fada ya ce lamarin mu’amamalar shi da maigidansa abin bai wuce kamar abokantakar mage da kare ba, saboda kowane lokacin suna cikin gardama na rashin biya kudin haya kan lokaci.
“Mai gidana ba ruwan shi da tausayi a irin halin da ake ciki a Nijeriya lokacin da kowa yake kokarin samun abin da zai ci. Sai ga shi yana kara kudin haya. Shi wani irin mutum mara tausayi. Kai ya yi ma duk abin da ya ga dama, domin ni ba ni da kudin da zan biya shi.”
Shi kuwa, Ebenezer Okonjo wanda yake zama a Ejigbo na Jihar Legas, yana ganin mai gidansa bai kyautawa, saboda yadda yake ta kara kudin haya yadda ya ga dama.
“Na fara hayar wannan gidan daga mahaifin maigidana lokacin yana Landan, yanzu da yake ya dawo bayan rasuwar babansa, abu na farko da ya yi min shi ne, kara kudin haya.
“Na fada masa ba zan iya biyan karin kudin hayar ba, sai ya ce mani in koma kauyena, saboda ita Legas ba an yi ta don kowa ba ne. Ni kuma na ga ba karamin cin mutunci ya yi mani ba. Sai na ce masa bai da tausayi, daga haka sai ya ban takarda cewa in fita daga gidansa, wadda na ki amsa. Tun wancan lokacin ne muka fara zaman doya da manja.”
Masu gidajen haya sun ce ba za ta sabu ba, su lale makudan kudade su gina gida domin su bayar da shi haya, amma dan haya ya kasa biyan kudin haya. Su kuma masu haya suna kokawa ne kan irin matsin tattalin arziki da ake ciki a Nijeriya wanda hakan ne ya sa ba su iya biyan kudin haya.