An shawarci Gwamnatin Kano karkashin shugabancin Injiniya Abba Ka-bir Yusuf, da sauran hukumomin kare hakin bil`adama da sauran masu ruwa da tsaki su gaggauta daukar mataki na haramta wa mata baza jari-rai a titinan jihar da sunan bara.
Wannan kiran ya fito ne daga bakin Sarkin Dilalan Kano, Ambasada Mustapha Abdullahi Aro a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Kano.
- Shekara Guda Bayan Zaben 2023: Har Yanzu Nijeriya Ba Ta Warware Ba
- Jimilar Kudin Da Sin Ta Samu Wajen Jigilar Kayayyaki A Farkon Watanni Biyu Na Bana Ta Kai Yuan Triliyan 55.4
A cewarsa, ya kamata daukacin al`umma su hada kai wajen daukar matakin haramta wa mata mabarata wannan mummunar dabi’a ta baza jariransu a rana a titinan Kano “kamar yadda duk mai bin titinan Kano zai ga wannan abu na ban tausayi da takaici.
“Babu dadi yadda mata mabarata ke baza jariransu a titinan Kano da sunan bara da kuma ‘yan mata kanana da suke kwararowa daga karka-ra da sunan goge motocin mutane a titinan Kano, wanda wannan ya sa-ba wa ka`idar addini da al`adarmu ta Jihar Kano.
“Kasancewar mu a jihar nan muna da tausayi da taimako daidai gwargwado, muna kira ga daukacin hukumomi su haramta irin wannan al`ada tare da kara kokarin inganta rayuwar jama’a.” Ya bayyana.
Har ila yau, Ambasada Mustapha ya nuna farin ciki da yadda Gwamna-tin Kano da mawadata suka amsa kira wajen taimaka wa al`umma a wannan watan na azumi, kana ya ce akwai bukatar al`umma ta rubanya aikin alkhairi a kodayaushe domin hakan zai taimaka wajen kawo arziki, zaman lafiya da kwamciyar hankali a Kano da Nijeriya baki daya.
Ya ba da tabbacin cewa a bangarensu na dillalai za su kara himmar tal-lafa wa marayu da kayan abinci da sutura tare da jaddada kira ga ma-hukunta kan tallafa wa matasa maza da mata a kan ilimi da sana’o’i.