• English
  • Business News
Sunday, August 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Taron Hadin Kan Maz’habobin Musulunci Ya Gudana A Saudiyya

by Yusuf Shuaibu
1 year ago
in Labarai
0
Yadda Taron Hadin Kan Maz’habobin Musulunci Ya Gudana A Saudiyya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Malaman addinin Musulunci sun gudanar da wani gagarumin taron hadin kai a tsakanin maz’habobi da darikun Musulunci a Makkah domin dinke baraka da rarrabuwar kai da ake samu a tsakaninsu.

Taron mai taken,“Gina gada tsakanin maz’habobin Musulunci da dariku”, ya samu halartar mabiya maz’habobi da darikun Musulunci daga ko ina a fadin duniya.

  • Hajjin Bana: Karin Naira Miliyan 1.9 Ya Jefa Dubban Maniyyata Cikin Garari
  • Mace Za Ta Iya Yin I’itikafi A Wannan Zamanin?

Kungiyar Kasashe Musulmi (MWL) ta shirya taron wanda Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz ya dauki nauyi. Malaman da suka halarci taron, sun bayyana aniyarsu ta inganta mu’amala domin farfado da gudunmawar da al’ummar Musulmi ke bayarwa wajen wayar da kan jama’a da samun ci gaba a duniya.

Shugaban kungiyar ta MWL, Mohammed Al-Issa, ya bayyana wani shiri da taron ya amince da shi na samar da daftarin da za a yi aiki da shi wajen tabbatar hadin kai a tsakanin maz’habobi da darikun Musulunci don tunkarar dimbin kalubalen da suka addabi Musulmi a duniya.

Haka kuma Al-Issa ya bayyana farin cikinsa da karbar bakuncin taron mai dimbin tarihi a Makkah tare da jaddada bukatar hadin kan al’ummar Musulmi.

Labarai Masu Nasaba

Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam’iyyar A Katsina

Sanata Shehu Buba Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Da Rigakafin Shanu A Bauchi

Sai dai ya yi gargadi game da kalaman bangaranci, ya kuma yi kira da a rika yada labaran da suka dace a kafafen yada labarai da ke kara samar da hadin kai. Ya mika godiyarsa ga mahukuntan kasar Saudiyya kan goyon bayan da suke ba su tare da yin addu’ar Allah ya kara ba su nasara.

A jawabinsa, Babban Mufti na Saudiyya, Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh, wanda Dakta Fahd Al-Majid ya gabatar, ya jaddada muhimmancin hadin kan al’ummar Musulmi, tare da tsawatarwa kan illar rarrabuwar kawuna kana ya bayyana irin gudunmawar da malamai ke bayarwa wajen samar da hadin kai a tsakanin Musulmai.

Ya gode wa Babban Hadimin Masallatai Masu Alfarma Guda Biyu, Sarki Salman Bin Abdulaziz kan goyon bayan taron tare da yaba wa kokarin hadin kan musulmai karkashin jagorancin Yarima Mohammed Bin Salman kuma Firayim Ministan Saudiyya.
Shi kuwa a nashi bangaren, Babban sakataren Kungiyar Hadin kan Musulmi (OIC), Hissein Brahim Taha ya yaba wa Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bisa goyon bayan shirya taron. Ya tabbatar da cewa muhimmin taron zai inganta hadin kai a tsakanin maz’habobi da darikun Musulunci tare da shawarwarin da za a yi amfani da su wajen samar da hadin kai da magance sabani.

Taha ya kuma yaba wa kungiyar MWL bisa sadaukarwar da take yi wa Musulunci da Musulman duniya baki daya.

A gefe guda kuma, an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin kungiyoyin MWL da OIC kan hadin kai.

An rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakanin Cibiyar Fikhu ta Musulunci ta MWL da Cibiyar Nazarin Fikhu ta kasa da kasa ta OIC domin bunkasa hadin gwiwa a fannin bincike.

Wasu malamai na ganin wannan taron zai cimma nasara, yayin da wasu ke ganin har yanzu da sauran rina a kaba.

Babban limamin masallacin rukunin gidaje na Lake Biew Phase 2 da ke Abuja, Malam Falalu Abdullahi ya bayyana cewa, tun lokacin da hukumomin Saudiyya suka dage dokar hana wadanda ba Musulmai shiga Harami ba suka sauka daga layi. Ya ce irin wannan taro ba zai samu nasara ba har sai mahukunta kasar sun dawo kan layi.

Yayin da shi kuwa, Malam Bello Abukakar ke da ra’ayin cewa lallai wannan taron zai samu nasara. Ya ce kiran mabiya maz’habobi da darikun Musulmi wurin guda da aka yi shi kansa babban nasara ce.

Ya kara da cewa yana da yakinin wannan taro zai samu nasarar hada kan al’ummar Musulmin duniya matukar kowane dan maz’haba zai amince da hadin kan Musulunci fiye da daukaka maz’haba ko darikar ko kungiyarsa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Mace Za Ta Iya Yin I’itikafi A Wannan Zamanin?

Next Post

Chelsea Za Ta Fafata Da Real Madrid Da Manchester City A Amurka

Related

Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam’iyyar A Katsina
Labarai

Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam’iyyar A Katsina

1 hour ago
Sanata Shehu Buba Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Da Rigakafin Shanu A Bauchi
Labarai

Sanata Shehu Buba Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Da Rigakafin Shanu A Bauchi

2 hours ago
Dangote Ya Ɗauki Nauyin Bikin Baje Kolin Gidajen Afrika Da Mahalarta Ƙasashe 21
Labarai

Dangote Ya Ɗauki Nauyin Bikin Baje Kolin Gidajen Afrika Da Mahalarta Ƙasashe 21

4 hours ago
Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar Da Hankali Kan Dakatar Da Gidan Rediyon Badeggi FM
Labarai

ADC Ta Yi Allah-wadai Da Rufe Gidan Rediyon Badeggi FM A Neja

9 hours ago
Gwamnatin Katsina Ta Gabatar Da Matsayarta A Taron Jin Ra’ayiyin Jama’a
Labarai

Gwamnatin Katsina Ta Gabatar Da Matsayarta A Taron Jin Ra’ayiyin Jama’a

10 hours ago
Borno Za Ta Sake Tsugunar Da ‘Yan Gudun Hijira 5,000 Kafin Damuna Ta Kare
Manyan Labarai

Borno Za Ta Sake Tsugunar Da ‘Yan Gudun Hijira 5,000 Kafin Damuna Ta Kare

11 hours ago
Next Post
Chelsea Za Ta Fafata Da Real Madrid Da Manchester City A Amurka

Chelsea Za Ta Fafata Da Real Madrid Da Manchester City A Amurka

LABARAI MASU NASABA

Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam’iyyar A Katsina

Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam’iyyar A Katsina

August 3, 2025
Sanata Shehu Buba Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Da Rigakafin Shanu A Bauchi

Sanata Shehu Buba Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Da Rigakafin Shanu A Bauchi

August 3, 2025
Waɗanne Ƙasashe Ne Suka Amince Da Kafa Ƙasar Falasɗinu?

Waɗanne Ƙasashe Ne Suka Amince Da Kafa Ƙasar Falasɗinu?

August 3, 2025
Dangote Ya Ɗauki Nauyin Bikin Baje Kolin Gidajen Afrika Da Mahalarta Ƙasashe 21

Dangote Ya Ɗauki Nauyin Bikin Baje Kolin Gidajen Afrika Da Mahalarta Ƙasashe 21

August 3, 2025
An Fara Bayar Da Hidimomin Da Suka Shafi Sauka Da Tashi Domin Gasar Wasanni Ta Duniya Ta Chengdu

An Fara Bayar Da Hidimomin Da Suka Shafi Sauka Da Tashi Domin Gasar Wasanni Ta Duniya Ta Chengdu

August 3, 2025
Rikici Ya Ɓarke A Zaɓen Ribas, Ƴan PDP Sun Fito A Matsayin Ƴan Takarar APC

Rikici Ya Ɓarke A Zaɓen Ribas, Ƴan PDP Sun Fito A Matsayin Ƴan Takarar APC

August 3, 2025
Ana Gaggauta Ayyukan Gyara Tituna Da Gadojin Da Ambaliya Ta Lalata A Arewacin Kasar Sin

Ana Gaggauta Ayyukan Gyara Tituna Da Gadojin Da Ambaliya Ta Lalata A Arewacin Kasar Sin

August 3, 2025
Shugabar Tanzania Ta Kaddamar Da Cibiyar Cinikayya Da Jigila Da Sin Ta Gina A Kasar

Shugabar Tanzania Ta Kaddamar Da Cibiyar Cinikayya Da Jigila Da Sin Ta Gina A Kasar

August 3, 2025
Manoma Sun Caccaki Tinubu Kan Ƙarfafa Shigo Da Shinkafa Da Masara Daga Ƙasashen Waje

Manoma Sun Caccaki Tinubu Kan Ƙarfafa Shigo Da Shinkafa Da Masara Daga Ƙasashen Waje

August 3, 2025
Amurka Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Zuwa Ƙasarta Domin Haihuwa

Amurka Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Zuwa Ƙasarta Domin Haihuwa

August 3, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.