Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna ta dakatar da shugabar matan jami’yyar, Maryam Suleiman, kan sukar gwamnan jihar, Uba Sani.
Takardar dakatarwa mai kwanan watan 31 ga watan Maris mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar APC da sakataren gundumar Badarawa/Malali, Ali Maishago da Zakkah Bassahuwa, ta ce an dakatar da shugabar matan ne bisa zargin bata sunan Gwamna Uba Sani, da kuma tada zaune tsaye a jami’yyar.
- Idan Aka Fatattaki ‘Yan Ta’adda Daga Zamfara Duk Arewa Za Mu Samu Sauki – Gwamna Dauda
- Sin Na Da Kananan Jirage Marasa Matuka Sama Da Miliyan 1.26Â
Ana zargin ta ne ta aike ‘yan daba su kai wa mai bai wa gwamna shawara kan harkokin siyasa, Manzo Maigari hari.
Takardar ta nuna cewa matakin da shugabar matan ta dauka ya saba wa sashe 21, 2 (v) na kundin tsarin jami’yyar APC.
A wani faifan bidiyo da ta yi cikin harshen Hausa, shugabar matan jam’iyyar APC ta soki kalaman Gwamna Sani kan dimbin bashin da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ta bari.
A jawabin da ya yi wa masu ruwa da tsaki a taron da aka gudanar a ranar Asabar, Gwamna Sani ya ce ya gaji bashin da ya kai dala miliyan 587, da Naira biliyan 85, da kuma bashin kwangilolin 115 daga gwamnatin El-Rufai.
Amma da ta ke mayar da martani kan kalaman gwamnan, shugabar matan jam’iyyar, ta zargi gwamna Sani da rashin iya gudanar da mulki da kuma dora laifi a kan El-Rufai.