‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mai juna biyu a yankin Lema daura da Mando kusa makarantar horon sojoji (NDA) da ke cikin jihar Kaduna.
Har ila yau, ‘yan bindigar sun kuma sace wasu mutane bakwai a gidajensu da suka shiga da misalin karfe 1 na daren jiya.
- Manyan Makaratun Jihar Bauchi Sun Ayyana Yajin Aikin Gargadi Na Mako 2
- ‘Yan Sanda Sun Damke ‘Yan Sane 6 a Jigawa
An ruwaito cewa, daya daga cikin mazuna yankin, Musa Danladi, ya sanar da cewa, dukkan mazauna yankin sun ji tsoron su fito daga gidajensu lokacin da ‘yan bindigar suka zo yankin saboda yadda ‘yan bindigar suka dinga harbi da bindiga.
Danladi ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun zo yankin ne da misalin 1 daya na dare, inda suka yi garkuwa da mutane takwas ciki har da mai juna biyu wacce ta zo yankin domin ta duba mahaifarta wadda ba ta da lafiya, inda ya kara da cewa wannan ne lokaci na farko da ‘yan bindigar suka shiga yankin.
Sai dai, har yanzu gwamnatin jihar ba ta yi wani jawabi kan lamarin ba haka kuma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, bai fitar da wata sanarwa kan harin na ‘yan bindigar ba.