Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi gargadi ga mazauna Abuja, Kano, da wasu jihohin Arewa da dama kan dumamar yanayi da ake kyautata zaton za ta afkawa yankin a ranar Asabar 6 ga Afrilu, 2024 kuma akwai yiwuwar al’ummar yankin su kamu da cutar sankarau.
Ciwon sankarau, wani yanayi ne mai barazana ga rayuwa wanda ke tasowa daga gazawar jiki wajen daidaita yanayin zafinsa, yana haifar da babban hadari ga al’ummar da ke fuskantar matsanancin zafi.
- Zaben Edo Da Ondo: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Gana Da Hukumar Zabe
- Wadanda Suka Wawashe Hatsi A Kebbi Sun Shiga Firgici Bayan Kwace Buhun Shinkafa 2,000
A cikin sabuwar gargadin da aka fitar ranar Juma’a, NiMet ta kasa jihohi 36 zuwa matakai biyar na haɗari.
Jihohi irin su Abuja, Kano, Sokoto, da Kogi na karkashin rukuni “Mafi girman haɗari.”
Jihohi kamar Kebbi, Katsina, Adamawa, duk sun shiga cikin jerin yankunan da ke fuskantar matsananciyar hadari, lamarin da ke kara nuna damuwa kan matsalolin kiwon lafiya a yankin.
Yayin da wasu jihohi da suka hada da Osun, Ekiti, da Ondo, ke karkashin tsarin “Tsawatarwa”, NiMet ta shawarci mazauna yankin da su kasance cikin taka-tsan-tsan
Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fama da zafin rana a Nijeriya tsawon makonni, inda yanayin zafi ya kai kusan 40°C a wasu yankuna.