A ranar Asabar da ta gabata, tun da sanyin safe matasa da mata da tsoffafi har da matan aure suka far ma sauran buhunan shinkafar Dangote da aka kai tallafi Jihar Kebbi inda suka wawashe akalla buhu dubu biyu.
Bayan samun wannan labarin abin da matasa da sauran jama’a suka aikata jami’an tsaro sun kawo dauki na gaggawa don ganin jama’a ba su wawashe shinkafar ba. Jami’an tsaro sun yi iya kokarisu wajen mai do da shinkafar da aka wawashe.
- Karin kudin Aikin Hajji: Gwamnatin Kebbi Za Ta Tallafawa Kowanne Maniyyaci Da Naira Miliyan 1
- Gwamnatin Kebbi Ta Amince Da Murabus Din Babban Limamin Masallacin Wala
Bayan aukuwar wannan ne, duk dai a ranar da misalin karfe daya na dare jama’a suka sake fitowa suka fasa rumbun ajiyar abincin da karamar hukumar Birnin Kebbi ta ajiye da zimmar rabawa ga jama’arta washe garin ranar Lahadi. A nan ma jami’an tsaron ‘yansanda da na Sojoji sun yi iya kokarinsu na ganin cewa jama’a basu wawashe dukkan abincin ba ta hanyar sanya barkonon tsohuwa amma duk da hakan bai hana aka wawashe wani sashe daga cikin abincin ba.
Yanzu hakan, a Jihar ta kebbi akwai labarin cewa jami’an tsaro sun samu nasarar cafke wasu daga cikin jama’ar da ake zargi da wawashe rumbun da kuma na wata mota a kusa dakasuwar kara da ke cikin garin Birnin Kebbi.
Ganin yadda abin ya auku bi da bi, sai ‘yansanda suka fantsama farautar mutanen da ake zargi da wawashe abincin. Bisa ga hakan hankalin jama’a a garin na Birnin Kebbi ya tashi, inda jama’a da dama suka shiga tsoro da farga.
Bugu da kari, bayan wuni daya an samu zaman lafiya a sassan Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi, sai kuma a washegari, dubban mutane ne suka tattara kansu tare da kutsawa cikin shagunan ‘yan kasuwa masu sayar da shinkafa da sauran hatsi iri-iri a unguwar Bayan-Kara, suka kwashe daruruwan buhuna.
Wani matashi, Abu Wanzan ya bayyana wa wakilinmu cewa, “yunwa da fatara ne suka sa jama’a suka kai hari kan wajen da ake ajiye abinci, haka kuma ba mu ji dadin yadda aka fara raba kayan abinci na baya-bayan nan da gwamnati ta sayo wa al’ummar jihar ba. Da yawa mazauna yankin garin Birnin Kebbi har yanzu ba su amfana da abincin da Gwamna Nasir Idris ya ce za a raba ma jama’a ba.”
Bisa abin da ya faru, ofishin mataimakin gwamnan jihar ya fitar da sanarwa, ta nuna rashin jin dadi game da lamarin tare da bayar da tabbacin cewa an dauki tsauraran matakan tsaro domin dakile sake afkuwar lamarin.
Hakazalika kwamishinan yada labarai da al’adu Alhaji Yakubu Ahmad Birnin Kebbi, ya sanar wa manema labaru da kafa kwamitin mutane 13 a karkashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar gona domin gudanar da bincike kan lamarin, wanda gwamnati ta bayyana a matsayin abin takaici da zargi.
Shi ma da yake jawabi ga manema labarai kwamishinan Ma’aikatar aikin goma da albarkatun kasa Alhaji Shehu Mu’azu ya bayyana cewa yawancin shinkafar da aka kwashe daga dakin ajiyar kaya dake Bayan-Kara mallakin karamar hukumar Birnin Kebbi ne a wani bangare na tallafin da gwamnatin jihar ta raba wa Kananan hukumomin 21na jhar.
Ya ce jami’an tsaro sun yi nasarar kwato buhunan abincin sama da 2,000 daga hannun jama’a tare da mayar da su inda aka ajiye su.
Alhaji Shehu Mu’azu wanda shi ne shugaban kwamitin binciken ya shaida wa manema labarai cewa an ba ‘yan kwamitinsa wa’adin kwanaki biyar daga ranar Litinin zuwa Juma’a domin su binciki musabbabin faruwar lamarin, da gano mutane ko kungiyoyin da ke da hannu tare da ba gwamnati shawara yadda ya kamata don kiyaye afkuwar lamarin.
A ranar Alhamis 21 ga watann Maris, ne Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya kaddamar da rabon tallafin abinci da suka hada da shinkafa, Dawa da sauran hatsi domin tausaya wa jama’ar jihar a watan Azumin Ramadan.
Bayan makonni kadan da ya kaddamar da rabon tallafin abincin ne kuma sai Gidauniyar Dangote ta bayyana nata rabon tallafin wanda daga bisani aka daka wawa a ragowar da ba a kai ga rabarwa ba ga al’ummar jihar.