Babbar kotun Jihar Kano, ta sanya ranar 17 ga watan Afrilu a matsayin ranar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, zai gurfana a gabanta kan tuhumar cin hanci da rashawa.
Babban lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan shari’a, Haruna Dederi ne, ya tabbatar da hakan, inda ya ce za a gurfanar da Ganduje ne tare da matarsa da wasu mutane shida.
- Jami’ar NOUN Za Ta Bai Wa Hafsatu Abdulwaheed Da Innocent Chukwuma Digirin Girmamawa
- Allah ya yi wa Jaruma Saratu Giɗaɗo (Daso) Rasuwa
Wadanda ake tuhumar sun hada da Abdullahi Umar Ganduje, Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd, da Lesage General Enterprises.
Gwamnatin Jihar Kano wadda ta fara tuhumar mutanen, ta bayyana shirinta na gabatar da shaidu 15 da za su tsaya a gaban mai shari’a Usman Na’aba na babbar kotun jihar.
“Gaskiya ne. Mun shigar da karar kuma za a fara zama a ranar 17 ga watan Afrilu, 2024,” in ji shi.
Dederi, ya bayyana muhimmancin rikon amana a harkokin mulki, inda ya ce, “Abin da shi (Ganduje) bai gane ba shi ne ba zai iya guje wa wanna rana ba, tabbas za ta zo, kuma hakan zai zama izina ga kowa, har da mu da muke cikin gwamnati yanzu.”
“Yana cewa ba za mu iya gurfanar da shi ba, ya manta cewa laifin na karkashin nau’in laifukan jiha ne,” in ji shi.
“Ba batun laifin tarayya ba ne, kuma mun shigar da kara a gaban mai shari’a Liman kan hakan.”