ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jami’ar NOUN Za Ta Bai Wa Hafsatu Abdulwaheed Da Innocent Chukwuma Digirin Girmamawa

NOUN Za ta yaye ɗalibai 22,175

by Sulaiman
2 years ago
NOUN

Jami’ar NOUN za ta bayar da digirin girmamawa na dakta ga wasu hamshaƙan ‘yan Nijeriya biyu, wato Hajiya Hafsatu M.A. Abdulwaheed da Cif Innocent Chukwuma, a ranar Asabar 13 Ga Afrilun 2024.

Mataimakin Shugaban jami’ar, Farfesa Olufemi A. Peters, shi ne ya bayyana haka a wajen taron manema labarai da ya yi a Abuja a ranar Litinin kan bikin yaye ɗalibai karo na 13 da jami’ar za ta gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

  • Kwamishinar Kidaya Ta Sadaukar Da Albashinta Na Shekara Don Karfafa Mata A Kaduna
  • Maganar Da Aka Taba Fada Min ‘Duk Marubuta ‘Yan Wuta Ne’ Ta Tsaya Min A Rai – Rukayya

Daraktan Yaɗa Labarai na jami’ar, Malam Ibrahim Sheme, ya faɗa a cikin takarda ga manema labarai cewa, ita dai Hajiya Hafsatu Abdulwaheed, ita ce mace ta farko a Arewacin Nijeriya da ta wallafa littafin hikaya, sannan sananniyar ‘yar gwagwarmaya ce mai rajin tallafa wa al’umma.

ADVERTISEMENT

Littafinta, So Aljannar Duniya, an wallafa shi ne a cikin shekarar 1974.

Shi kuma Cif Chukwuma, shahararren ɗan kasuwa ne wanda ya assasa Innoson Motors, wanda shi ne kamfanin harhaɗa motoci na farko na ‘yan ƙasa da aka kafa a Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

A taron manema labaran, Farfesa Peters ya ce, za a ba Hajiya Hafsatu Abdulwaheed digirin girmamawa na Daktar Wallafa ne (wato Doctor of Letters, honoris causa).

Ya ce: “Ta sadaukar da rayuwar ta ga hidimar haɓaka harkar ilimi, musamman na ‘ya’ya mata, bisa amanna da cewa, iya karatu da rubutu yana da ƙarfin sauya matsayin al’umma tare da karya lagon fatara da yunwa.”

Shi kuma Shugaban kamfanin Innoson Motors za a ba shi digirin ne a fannin Gudanarwar Kasuwanci (Business Administration) saboda ya ciri tuta a fagen “ƙirƙira, assasawa, tare da sadaukarwa ga amfani da kayan aiki na cikin gida.”

Ya ƙara da cewa ayyukan waɗannan mutane biyu da za a karrama “sun yi daidai da ainihin burukan NOUN na asali na haɓaka ilimin kasuwanci, samar da ababen ilimi, da kuma ƙirƙira.”

Jagoran jami’ar ya yi nuni da cewa NOUN ba ta cika bayar da digirin girmamawa ba, domin na ƙarshe da ta bayar tun cikin 1995 ne, saboda haka sai da ta yi zurfin tunani kafin ta yanke irin wannan shawarar.

Peters ya ce wannan girmamawar da za ta yi babbar nasara ce ga al’ummar jami’ar kuma hanya ce da za a samar da kyakkyawan haɗin gwiwa da ya ginu kan harkar ilimi.

Haka kuma jagoran ya bayyana cewa a bikin na bana jami’ar za ta yaye ɗalibai 22,175 waɗanda daga cikin su guda 15,768 masu digirin farko ne daga tsangayu takwas na jami’ar, sai 6,407 masu digiri na biyu, da ɗalibai shida masu digiri na uku.

Kafin ranar Asabar da za a yi bikin, za a ƙaddamar da sabon Shugaban Jami’a, wato Oba na Benin, Oba Ewuare II, a ranar Alhamis, kuma za a yi taron laccar yaye ɗalibai wadda Mataimakin Shugaban Buɗaɗɗiyar Jami’ar ƙasar Tanzaniya, Farfesa Elifas Bisanda, zai gabatar a ranar Juma’a.

NOUN
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

MASU ALAKA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa
Labarai

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Next Post
Za A Gurfanar Da Ganduje A Kotu Kan Zargin Cin Hanci Da Rashawa A Kano

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.