Gwamnatin Jihar Katsina ta yi wa fursunoni 222 da suka gaza biyan tarar da kotuna daban-daban ta yanke musu afuwa, gabanin sallah a jihar.
Da yake yaba wa gwamna Radda kan wannan shiri, babban mai shigar da kara na Katsina ya bayyana cewa, an zabo wadanda suka ci gajiyar shirin ne, daga cikin fursunonin da ake tsare da su bisa kananan laifuka.
- Ana Fatan Amurka Za Ta Sauke Nauyin Dake Wuyanta Bayan Ziyarar Janet L. Yellen A Sin
- Eid-el-fitr: Gwamnatin Tarayya Ta Tsawaita Hutun Bukukuwan SallahÂ
Gwamnan jihar, Dikko Umaru Radda, ya ce manufar shirin, ita ce rage yawan fursunoni a fadin gidajen gyaran hali na jihar da kuma albarkacin watan Ramadan.
Babban lauyan jihar kuma kwamishiniyar shari’a, Fadila Muhammad Dikko ce, ta bayyana hakan a wata sanarwa.
Ta ce mutane 222 ne aka yi wa afuwa, an zabo su ne bayan an tantance su.
“Ana sa ran aikin alherin da gwamna ya yi zai rage cunkoso a wadannan wuraren tare da bai wa fursunonin da aka sako damar cin moriyar bikin sallah tare da ‘yan uwansu,” in ji Fadila.