• English
  • Business News
Saturday, June 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sallah Ƙarama: Abun Da Ya Kamata Ku Sani Kan Sallar Idi Da Ladubanta

by Nuhu Ubale Ibrahim
1 year ago
in Bakon Marubuci, Fatawa, Ilimi
0
Sallah Ƙarama: Abun Da Ya Kamata Ku Sani Kan Sallar Idi Da Ladubanta
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Yabo da godiya da kirari da girmamawa sun tabbata ga Allah shi kaɗai. Yabon Allah da amincinsa su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta shugaban farko da na ƙarshe tare alayensa da sahabbansa baki ɗaya.

Bayan haka; wannan rubutu ya ƙunshi bayani a kan sallar idi a bisa fahimtar Mazhabar Malikiyya. Ga bayanin kamar haka.

  • Sallar Idi Babbar Rana Ga Musulmi
  • Hukunce-Hukuncen Sallar Idi Da Zakatul Fidir

1. Sallar idi sunna ce mai ƙarfi ta wajibi.

2. Liman da mamu za su tafi filin idi bayan rana ta fito domin suna isa filin idi hantsi ya yi sai a yi sallah.

3. Ana yin sallar idi a filin idi ba a masallaci ba, sai dai idan akwai lalura, to za a iya yi a masallaci, haka nan waɗanda suke a garin Makka za su yinta a Harami.

Labarai Masu Nasaba

Gwamnatin Kano Ta Ba Da Hutun Makaranta Domin Bukukuwan Sallah

SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (3)

4. Mustahabbi ne mutum ya yi wanka domin sallar idi.

5. Mustahabbi ne idan an yi wankan a tafi masallaci ba tare da ɓata lokaci ba.

6. Mustahabbi ne a yi ado a sanya turare da sababbin tufafi ga wanda yake da iko.

7. Za a tafi filin idi ana kabarbari a bayyane har a je filin idi, idan an je ba a yin nafila, za a zauna a ci gaba da kabarbari har liman ya ƙaraso, sai a tsaya da kabarbari. Idan liman yana kabarbari, nan ma mamu za su yi kabarbari idan liman ya yi.

TAMBIHI: Kabarbari aka fi buƙata sama da wa’azi kafin liman ya zo, don Allah a bar al’umma su raya kabarbarbari a wurin idi.

8. Sallar idi raka’a 2 ce , kuma ana yin karatu a bayyane, a raka’a ta farko ana yin kabbara bakwai har da kabbarar harama sai liman ya fara karatu, a ta biyu kuma kabbara shida har da ta mikewa. Ana karanta Fatiha da Sabbi a rakar farko, a ta biyu kuma Hal’ataka ko kuma makamantansu.

9. Idan mutum bai riski wani abu tare da liman ba a raka’a ba, to, zai yi kabbara bakwai a raka’a ta farko kafin ya yi karatu, kuma zai kabbara shida a raka’a ta biyu kafin ya fara karatu kamar yadda liman ya yi.

10. Ba a yin nafila bayan an gama sallar idi.

11. Liman zai yi huɗuba guda biyu kuma zai zauna a tsakaninsu kuma ana so ya yawaita kabarbari a huɗubarsa.

12. Ana so a yi sallar layya da wuri a kan ta sallar azumi, domin ana so a ci abinci kafin a tafi karamar salla, ita kuma ta layya sai bayan an dawo.

13. Kabarbari da ake so a yi, laffuzansu suna da yawa kuma za a iya yin kowanne, daga ciki akwai: Allahu Akbar Allahu Akbar La’ilaha illallahu Allahu Akbar Allahu Akbar Walillahil Hamdu.

14. Ana so a rinƙa kabarbari a bayan kowacce sallar farilla sau uku har zuwa bayan salla da kwana uku, kuma ana so a yawaita zikiri a cikinsu.

15. Mustahabbi ne ga mata da yara idan ba za su je sallar idi ba, to su yi wanka da ado da sanya sababbun kaya idan da hali.

16. Mata su guji caba ado da sanya turare idan za su je idi saboda gudun fitina.

17. Makruhi ne mutum ya ƙi yin ado da kwalliyya da gayu a ranar idi wai don gudun duniya, idan kuma ya ƙi yi da sunan addini, to ya zama ɗan bidi’a.

18. Yara da mata za su iya yin wasanni a ranakun idi.

19. Mustahabbi ne mutum ya sabunta hanya wajen dawo wa gida daga idi, wato ya sauya hanya.

Allah ya karɓa mana ibadunmu, ya gafarta mana. Amin.

Manazarta:

1~ Muwadda Maliki [shafi 87-90] bugun Mu’assatul mukhtar.
2~ al-Mudauwanatul Kubra [1/223-231] ta Imam Malik Riwayatu Imam Hasnun, bugun Maktabatus Sakafati Addiniyyati.
3~ ar-Risãlatu [shafi na 71-72] na Abu Zaid al-Ƙairawãnī,bugun Dãrul Fadīlati.4~ at-Talƙīnu [shafi na 115-116] na Abdulwahab Albagdadi, bugun Dãrul Fadīlati.

5~ al-Ma’ūnatu [1/233-237] na Abdulwahab Albagdadi,  bugun Dãrul Fadīlati.
6~ al-Kãfi [shafi na 128-129] na ibnu Abdilbarri,  bugun Assahwatu.
7~ Mukhtasul Khalil [shafi na 87] na Shehu Khalil, bugun Dãru Ibnil Jauzī.
8~ Sharhul Iziyyati [shafi na 103-106] na Sharnūbi.

9~ Fathu Rabbil Bariyyati [shafi n 558-566] na Masur Sokoto, bugun Maktabatul Imamil Bukhari.
10~ Sirãjus Sãliki [1/135-137] na al-Ujali, bugun Dãrul Fikr11~ Bulgatus Sãliki [1/175-177] na Ahmad as-Sãwi, bugun Dãrul Fikr

13. Assharhu Assagir [1/652-660] na Ahmad ad-Dardir, bugun Dãrul Fadīlati.

14~ Taƙribul Murãdi [shafi na 124-128] na Sulaiman Zamfara, bugun Dãrul Ummati.

15. Jawãhirul Iklil [1/101-104] na Saleh Abdussami’i, bugun Sharikatul-ƙudsi.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: IdiKaramar SallahSallah
ShareTweetSendShare
Previous Post

Firaministan Kasar Sin Ya Jagoranci Taron Neman Ra’ayi Kan Aikin Tattalin Arziki

Next Post

Sallah: Ganduje Ya Bukaci Musulmai Su Yi Wa Nijeriya Addu’a

Related

Gwamnatin Kano Ta Ba Da Hutun Makaranta Domin Bukukuwan Sallah
Ilimi

Gwamnatin Kano Ta Ba Da Hutun Makaranta Domin Bukukuwan Sallah

6 days ago
SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (3)
Bakon Marubuci

SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (3)

6 days ago
Wasu ‘Yan Siyasa Da Jami’an Tsaro Na Taimaka Wa Boko Haram – Zulum
Ilimi

Zulum Ya Ba Da Tallafin Karatu Ga Mata ‘Yan Asalin Jihar Da Suka Samu Maki 250 A JAMB

7 days ago
Bayan Biyan Basussuka: WAEC Da NECO Sun Saki Samakon Jarrabawar Jihar Zamfara
Ilimi

Bayan Biyan Basussuka: WAEC Da NECO Sun Saki Samakon Jarrabawar Jihar Zamfara

7 days ago
Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (3)
Ilimi

Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (3)

7 days ago
Ɗalibai Sun Rubuta Jarrabawar WAEC Cikin Dare A Duhu
Ilimi

Ɗalibai Sun Rubuta Jarrabawar WAEC Cikin Dare A Duhu

1 week ago
Next Post
Sallah: Ganduje Ya Bukaci Musulmai Su Yi Wa Nijeriya Addu’a

Sallah: Ganduje Ya Bukaci Musulmai Su Yi Wa Nijeriya Addu'a

LABARAI MASU NASABA

Manchester City Ta Kammala Daukar Tijjani Reijnders Daga AC Milan

Manchester City Ta Kammala Daukar Tijjani Reijnders Daga AC Milan

June 7, 2025
Ban Sa Ran Lashe Kyautar Ballon D’or Ta Bana Ba – Lamine Yamal

Ban Sa Ran Lashe Kyautar Ballon D’or Ta Bana Ba – Lamine Yamal

June 7, 2025
Dangote Ya Sanya Wa Hanya Sunan Tinubu, Zai Kashe Naira Biliyan 900 Don Gina Hanyoyi A Nijeriya

Dangote Ya Sanya Wa Hanya Sunan Tinubu, Zai Kashe Naira Biliyan 900 Don Gina Hanyoyi A Nijeriya

June 7, 2025
Neja

Dalilin Rashin Fara Aikin Kamfanin Takin Zamani Na Gwamnatin Jihar Neja

June 7, 2025
Adawa

Yadda Rarrabuwar Kawunan Jam’iyyu Zai Iya Sauya Alkiblar Zaben 2027

June 7, 2025
2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

June 7, 2025
Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

June 7, 2025
Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe

Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe

June 6, 2025
Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Wajen Inganta Amfani Da Ruwa A Shekarar 2024

Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Wajen Inganta Amfani Da Ruwa A Shekarar 2024

June 6, 2025
Daurarru

Kashi 70 Na Fursunonin Nijeriya Ba A Yanke Musu Hukunci Ba

June 6, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.