Mahukuntan kasar Sin sun fitar da kundi mai kunshe da tsare-tsaren karfafa samar da tallafin kudade, domin ingiza ci gaba maras gurbata muhalli, da rage fitar da iskar carbon mai dumama yanayi.
Kundin wanda wasu sassan gwamnatin kasar ta Sin, ciki har da bankin al’ummar Sin ko PBOC suka fitar, ya bayyana aniyar kasar ta gina tsarin samar da tallafi irin na zamani, wanda cikin shekaru biyar masu zuwa zai ingiza bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da kara daidaita aiwatar da manufofi, da sanya su zama masu inganci da karko nan zuwa shekarar 2035, inda karkashin hakan za a shigar da karin albarkatu, da aiwatar da ayyukan kare hadurra, da lura da farashin kasuwa.
- Yawan Motocin Da Sin Ta Sayar Ya Kai Miliyan 6.72 A Rubu’in Farkon Bana
- An Amsa Tambayoyi Game Da Ziyarar Da Sakatariyar Baitil-malin Amurka Ta Gudanar A Sin
Kundin ya ce za a kara azamar fadada sassan cinikayya, wadanda za su ingiza ci gaban kasuwar carbon ta Sin, da kara yawan kudaden lamuni na tallafawa ci gaba maras gurbata muhalli, da sauya akalar ci gaban makamashi zuwa mafi karancin fitar da iskar, da raya masana’antu, harkokin sufuri, da gine gine da sauran fannoni, tare da tallafawa kamfanonin da suka cancanta, wajen samun rajistar gida da ta ketare don samun kudaden gudanarwa a matakai daban daban.
Har ila yau, kundin ya zayyana matakai da za a bi wajen kara kyautata dokoki da ka’idoji, na bunkasa auna nasarar shirin samar da kudade domin wadannan ayyuka, da matakan auna tasirin manufofi, da kyautata sassan manufofin kudi masu nasaba da shirin, da zurfafa sauye sauye a tsarin samar da kudade domin wannan muhimmin aiki a matakin shiyya. (Saminu Alhassan)