Adadin motocin da kasar Sin ta sayar a rubu’in farko na bana ya karu da kashi 10.6 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin na bara zuwa miliyan 6.72, kamar yadda kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin ta bayyana a yau Laraba.
A cikin watan Maris kadai, cinikin motocin da aka yi ya zarce guda miliyan 2.69, wanda ya karu da kashi 9.9 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin na bara. (Mai fassara: Yahaya)
Talla