Kungiyar masu masana’antu na Jihar Legas ta nuna damuwarta a kan yadda harkokin gudanar da kaswuanci ke ci gaba da hauhawa a Nijeriya, musamman karin kudin ruwan banki da aka yi kuma karin kudin wutar lantarki da aka yi kwanan nan.
Shugaban kungiyar, Dr. Chinyere Almona ta sanar da haka a takardar manema labarai da ta aikawa kamfanin buga jaridar LEADERSHIP.
- Ana Gudanar Da Horo Kan Gina “Koren Babbar Ganuwa” A Afirka A Beijing
- Jiga-jigan APC Da Ke Tsammanin Samun Mukamin Siyasa A Gwamnatin Tinubu Sun Shiga Rudani
Dr Aloma ta ce, sun nuna matukar damuwarsu a kan shawarar Babban Bankin Nijeriya na kara kudin ruwan karbar bashi daga bankunan Nijeriya daga Kashi 22.75 zuwa kashi 24.75, “Haka kuma mun yi tir da karin kudin wutar lantarki da aka yi kwanan nan hakan ya kara ta’azzara halin gudanar da raywua da kuma gudanar da harkokin kaswuanci a Nijeriya.” In ji ta.
Ta lura da cewa, wadannan shawarar sun kara wahala a wurin shigo da kayayyaki daga tashohin jiragen ruwan Nijeriya, haka kuma rashin tsayar da darajar naira yana hana duk wani kokari na yadda za a shirya yadda za a gudanar da kasuwancinsa na dan wani lokaci mai tsawo, bayanan da muka samu daga ‘yan kasuwua ya nuna cewa suna fuskantar matsaloli wajen gudannar da kasuwanci kuma babu riba a harkar kasuwanci a wannan lokacin gaba daya.”
Daga nan ta ce, a halin yanzu bangaren masana’antu masu zaman kansu wadanda sune kashin bayan kowanne tattalin arziki suna fuskantar kalubalen yadda za su ci gaba da harkokinsu saboda tsadar ruwan banki, raguwar masu zuba jari da kuma rashin tabbas a tsare-tsaren tattalin arzikin kasa.
A kan haka suka nemi CBN ya sake duba wadanna tsare-tsaren da nufin yi musu gyaran da ya kamata, ta haka za a samu tabbacin farfadowar tattalin arzikin kasa a cikin dan lokaci mai zuwa.