Yau Jumma’a, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta gudanar da taron manema labarai. Game da wasu kasashen kudancin Afirka masu fuskantar bala’in fari, kakakin ma’aikatar Mao Ning ta bayyana cewa, bangaren Sin ya dade yana kula da bala’in fari da karancin abinci da kasashen suke fuskanta, tana shirya ayyukan samar da tallafin abinci na gaggawa ga kasashen Afirka fiye da 20 da suka hada da Zimbabwe da Malawi da Zambiya.
Game da batun da zuba jarin Sin ga makamashi na bola-jari a kasashen Afirka, Mao Ning ta ce, Sin ta riga ta gudanar da daruruwan ayyukan makamashi mai tsabta da na ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a nahiyar Afirka, Sin ta dade tana goyon bayan kasashen Afirka wajen samun ci gaba mai dorewa.
- Sin Na Goyon Bayan Yunkurin IAEA Na Tabbatar Da Tsaron Tashar Nukiliya Ta Zaporizhzhia
- Sin Na Goyon Bayan Yunkurin IAEA Na Tabbatar Da Tsaron Tashar Nukiliya Ta Zaporizhzhia
Game da bashin kasashe masu tasowa, Mao Ning ta bayyana cewa, bangaren Sin ya dora muhimmanci sosai kan batun bashin kasashe masu tasowa, a ko da yaushe yana bin ka’idar tattaunawa cikin daidaito da samu nasara tare ta hadin gwiwa, tare da taimaka saukaka nauyin bashi dake wuyan kasashe masu tasowa, da kuma inganta ci gaba mai dorewa.
Game da tattaunawar da ministan wajen Sin Wang Yi ya yi ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken jiya Alhamis bisa gayyata, Mao Ning ta ce, bangren Sin ya yi Allah wadai da hare-haren da aka kai wa ofishin jakadancin Iran dake Syria, kuma ya yi alkawarin cewa, zai ci gaba da ba da gudummawa ga warware rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.
Game da batun cewa Amurka za ta karfafa dangantaka tsakaninta da Japan da Philippines a kan harkokin teku, Mao Ning ta ce, bangaren Sin ba zai sauya aniyarsa wajen ci gaba da kiyaye ikon mallakar kasa da iko da moriyar tekunsa ba, sannan ya nuna adawa da tsoma bakin da kasashen suke yi don tada rikici.(Safiyah Ma)