• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasashen Ghana Da Kenya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Hadin Gwiwa

by Rabi'u Ali Indabawa
2 years ago
Ghana

Shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo-Addo da na Kenya, William Ruto, sun shaida hakan inda Ministar harkokin wajen Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey, da sakataren majalisar ministocin harkokin wajen Kenya, Dokta Musalia Mudabadi, suka jagoranci rattaba hannun.

Kasar Ghana da Kenya sun kara habaka huldar diplomasiyya da tattalin arziki, ta hanyar rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da za ta tabbatar da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da burin nemo hanyoyin da kasashen za su bunkasa huldar kasuwanci, tattalin arziki da zamantakewa a tsakaninsu.

  • An Bude Baje Kolin Kayayyakin Masarufi Na Kasa Da Kasa Na Sin Karo Na 4
  • Cinikayyar Shige Da Fice Ta Sin Ta Daga Da Kaso 5% A Rubu’in Farko Na Bana

Kasashen biyu sun rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi 7 da suka hada da ilimi, yawon bude ido, tsaro, da inganta zuba jari, masana’antu, kere-kere da kasuwanci, a yayin ziyarar kwanaki uku da shugaban kasar Kenya, William Ruto, ya kai zuwa Ghana.

Shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo-Addo da na Kenya, William Ruto, sun shaida hakan inda Ministar harkokin wajen Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey, da sakataren majalisar ministocin harkokin wajen Kenya, Dokta Musalia Mudabadi, suka jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar diflomasiya a fadar Shugaban Kasa, Jubilee House, dake Birnin Accra.

Haka kuma an rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi da suka hada da ilimi, yawon bude ido, hadin gwiwa kan tsaro, kasuwanci da zuba jari, masana’antu da gudanar da mulki domin karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu.

LABARAI MASU NASABA

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

A wani taron manema labarai na hadin gwiwa, shugaba Akufo-Addo ya ce, ‘Huldar kasuwanci da tattalin arziki tana ci gaba da bunkasa a tsakanin kasashen Ghana da Kenya, inda kasashen biyu ke kara fahimtar juna da kuma nuna goyon baya ga juna a kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Afirka, da Kungiyar Kasashen Renon Ingila, na Commonwealth’.

A nasa bangaren Shugaba Ruto ya bayyana cewa, ‘yancin zirga-zirgar jama’a tsakanin Ghana da Kenya ya haifar da fa’ida sosai a fannin kasuwanci, zuba jari, da kuma yawon bude ido.

“A dangane da haka, ni da mai girma shugaban kasa, mun lura cewa, kasuwanci tsakanin Kenya da Ghana ya bunkasa a shekarar 2022, misali, a shekarar 2022, Kayayyakin da Kenya ta shigo da su cikin Ghana sun kai na Dalar Amurka miliyan 10.4, kuma an kiyasta wasu kayayyakin da ake shigo da su a kan Dalar Amurka miliyan 4.8.”

Wani mai sharhi kan harkokin siyasar cikin gida da ketare, Malam Issah Abdul Salam yace,sakamakon alaka da aka dora tsakanin Ghana da Kenya, ya sa shugaba William Ruto ya zo Ghana don kara jaddada alaka mai kyau da ke tsakaninsu tun da jimawa. Kuma wannan ziyarar za ta aka kara bunkasa sha’anin, ‘ilimi, yawon bude ido da ba da dama ga ziyarar kasashen juna, abubuwa ne da za su samar da mafani masu dimbin yawa tsakanin Ghana da Kenya”.

Masani kan harkokin kudi da kasuwanci, Hamza Attijjany, ya ce kasashen biyu za su amfana ta bangaren tattalin arziki, musamman a kasuwanci da bas hi da shinge tsakanin kasashen Africa, da kasar Ghana da Kenya suka runguma da hannu biyu-biyu.

Ya ce, ‘A lokacin da kasar Kenya ta fara yin batir, Ghana ce kasa ta farko da aka fara yi wa talla don kasuwanci. Lallai Ghana da Kenya za su samu ci gaban tattalin arziki da ma nahiyar Afirka baki daya’.

Al’ummar kasashen biyu, za su samu alfanu idan an tabbatar da wadannan yarjejeniyoyin, in ji mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Malam Issah Mairago Gibril Abbas,wanda ya ce daliban kasashen biyu za su samu damar zurfafa iliminsu ta hanyar yarjejeniyar; haka kuma ‘yan kasuwar kasashen za su ci moriyar shirin nan na cinikayya tsakanin kasashen Afrika mara shinge AfCFTA.

A yayin ziyarar shugaba Ruto, ta kwanaki ukun, ya ba da lecca a shalkwatar AfCFTA ya kuma ziyarci kabarin tsohon shugaban Ghana, Kwame Nkrumah, a Birnin Accra. Daga bisani Ghana ta karrama shi da babbar karramawa mai daraja, wato Companion of the Order of the Star of the Bolta.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi
Labarai

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza
Labarai

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar
Labarai

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Next Post
Jinyar Wata 7: Babu Abin Da Zan Ce Ga Masoyana Sai Godiya -Malam Na Ta’ala

Jinyar Wata 7: Babu Abin Da Zan Ce Ga Masoyana Sai Godiya -Malam Na Ta'ala

LABARAI MASU NASABA

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

October 19, 2025
Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

October 19, 2025
Yadda Ake Alkaki

Yadda Ake Alkaki

October 19, 2025
Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (2)

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.