A wajen taron cudanyar wayewar kai na Sin da Afirka karo na 3, da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin a kwanan baya, darektan cibiyar nazarin harkokin ci gaban kasa ta kasar Uganda, kuma babban mai nazari, Allawi Ssemanda, ya yi jawabi, inda ya ambaci batun shafawa huldar dake tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin kashin kaza, da wasu kafofin watsa labaru na kasashen yamma suka dade suke yi. Ya ce, “A duk lokacin da kafofin yada labaru na kasashen yamma suka yi magana kan hadin gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin, kusan ba su taba ambatar yadda ake hadin gwiwa don amfanin juna ba, maimakon haka su kan yada wasu karairayin cewa, Sin na dana ‘tarkon bashi’, ko kuma ‘kasar Sin za ta yi mulkin mallaka a kasarku’.”
Hakika, a shekarun baya, yayin da ake ta samun rikice-rikice a duniya, kasar Amurka da wasu kawayenta na yammacin duniya suna kara shafa wa hadin gwiwar Sin da Afirka da kashin kaza, kuma ta hanyoyi daban daban. Alal misali, cibiyar nazarin manufofin raya kasa na duniya ta jami’ar Boston ta kasar Amurka, ta gabatar da wani rahoton bincike a kwanan baya, inda ta yi suka kan jarin da kasar Sin ke zubawa kasashen Afirka, cewa wai “kasar Sin ba ta mai da hankali kan zuba jari ga bangaren makamashin da ake iya sabuntawa a kasashen Afirka ba”.
- Babban Layin Tashar Wutar Lantarki Na Kasa Ya Sake Faduwa
- Babban Layin Tashar Wutar Lantarki Na Kasa Ya Sake Faduwa
Sai dai wannan magana sam ba gaskiya ba ce. Idan mun dauki aikin raya makamashi mai tsabta a kasar Najeriya a matsayin misali, za mu ga yadda kamfanonin kasar Sin suka zuba jari gami da daukar nauyin gina madatsar ruwa ta Zungeru, wadda ta fi girma a kasar Najeriya. An ce wutar lantarkin da madatsar ruwan ke samarwa za ta iya biyan bukatun babban birni irinsa Abuja guda 2.
Hakika a shekarun baya, kasar Sin ta riga ta aiwatar da daruruwan ayyukan raya makamashi mai tsabta, da na bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, a nahiyar Afirka, ta yadda take kan gaba a duniya ta fuskar hadin kai da kasashen Afirka a wadannan fannoni. Misali, a kasar Morocco, tashar samar da wutar lantarki ta zafin hasken rana ta Noor, da wani kamfanin kasar Sin ya gina, tana samar da wutar lantarki mai tsabta ga magidanta fiye da miliyan 1, ta yadda aka canza yanayin da kasar Morocco ke ciki na dogaro kan wutar lantarki na kasashen waje. Kana a kasar Afirka ta Kudu, tashar samar da wutar lantarki ta karfin iska ta De Aar, da wani kamfanin Sin ya zuba jari gami da gina ta, ta kan samar da wutar lantarki da yawanta ya kai KWH miliyan 760 duk shekara, don biyan bukatun magidanta dubu 300. Ban da haka, a kasar Uganda, ba a jima da kammala aikin kafa na’urar samar da wutar lantarki na karshe ba, a tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa ta Karuma, da wani kamfanin kasar Sin ya gina, matakin da ya sa karfin samar da wutar lantarki na kasar ya karu da kimanin kashi 50%.
To, sai dai me ya sa kasar Amurka da kawayenta na yammacin duniya ke son shafawa kasar Sin da huldar hadin gwiwa dake tsakaninta da kasashen Afirka da kashin kaza? A cewar Allawi Ssemanda, “ Kasashen yamma suna kallon kansu kamar masu gida ne, wadanda suka fi ilimi. Saboda haka suna son shawo kan sauran kasashe. Kana sun cika girman kai inda suke ganin cewa duk wani abu mai amfani, sai daga wajensu ne zai iya fitowa.”
Sai dai yaya aikin “shawo kan” sauran kasashe da kasar Amurka da kawayenta suke? Allawi Ssemanda ya ce, “ Dukkan kasashen Afirka sun tuna yadda kasashen yamma suka tilasta musu, don su gudanar da shirin daidaita tsare-tsaren tattalin arizki, tare da zummar gurgunta su. ” Yana nufin gyare-gyaren da kasashen yamma suka tilastawa kasashen Afirka don su yi, ta bankin duniya, da hukumar ba da lamuni ta duniya, tun daga tsakiyar shekarun 1970, wadanda suka shafi matakan raba dukiyoyin gwamnati ga masu jari hujja, da samar da ’yanci ga ayyukan zuba jari da ciniki, da dai sauransu. Matakan da suka haddasa koma bayan tattalin arzikin kasashen Afirka, da faduwarsu cikin tarkon bashi na gaske.
Ban da haka, Mista Ssemanda ya ce, “Akidar ’yanci ta Liberalism ta kasashen yamma ba wata daidaitacciyar akidar siyasa ba ce, maimakon haka, ta kasance wani karfi ne dake neman yin habaka a kai a kai.” Wannan ra’ayinsa ya samu karin tabbatarwa daga wata masaniyar ilimi mai alaka da kasashen Afirka ta kasar Sin Liu Haifang. Wani kundin da ta rubuta ya nuna cewa, akidar ’yanci ta kasashen yamma ta sa kasashen Afirka shigar da dimbin jari daga kasashen waje ba tare da wata kayyadewa ba, abin da ya sa kasashen Afirka zama ’yan amshin shatar sauran bangarori. Inda masu jari suka hada baki da masu iko dake wurare daban daban, da wadanda ke wakiltar wasu kabilu, da addinai, don kafa dimbin gungun dake neman kare moriyar kansu. Hakan ya sa aka samu ikon tabbatar da manufofin kasa, da sanya dimbin kasashe dake nahiyar Afirka rasa karfin kare moriyar kasa.
Da wannan za mu san cewa, ra’ayin wani yana da alaka da matsayinsa. Idan an dauki matsayi na kasashen yamma, za a yi tsammanin cewa, duk wani matakin da kasashe masu tasowa suka dauka ba zai yi daidai ba, ban da hakuri da ci da gumi da bautarwa da kasashen yamma suka yi musu. Saboda haka dole ne kasashe masu tasowa su dauki matsayi na kansu, da kokarin kare moriyar kasa, da tantance abubuwa bisa yanayi na gaske da suke ciki, ta yadda za a iya samun daidaitaccen ra’ayi, tare da daukar matakai masu dacewa. (Bello Wang)