Ko dan jariri da ke cikin mahaifiyarsa ya san irin alkaba’in da ke addabar duniya a halin yanzu ta fuskar tabarbarewar tsaro. Tsoro da firgici na ci gaba da haifar da razani a tsakanin al’umma. An mayar da kwararar da jinin Bil’adama ba a bakin komi ba. Ana kashe mata da kananan yara, haka nan tsofaffi da dattawa duk babu wanda ya tsira. Dokokin kiyaye kisan kare-dangi tamkar ba su aiki saboda munafurcin Turawan yamma. Wanda suke so shi ne da gaskiya komai zaluncinsa wanda ya zamo dan adawarsu kuwa shi ne tunku-uwar-laifi duk irin gaskiyarsa.
Tauye ‘yancin kasashe masu cin gashin kansu ya yawaita, karfafa abokan hulda masu tayar da zaune tsaye a kasashen da suka ki bayar da kai bori ya hau ya zama ruwan dare game da duniya. Duk wadannan abubuwa an gan su a Zahiri sun faru a Iraki, Libiya, Venezuela da wasunsu da dama. Sai kuma rikicin cikin gida da ake rurawa da kusan yau a duniya kasashe daidai ne suka tsira daga makircin su Amurka kan haka.
Al’ummar duniya ta gaji da alkaba’in rashin tsaron da ake fama da shi, wanda wani lokaci mutumin da yake rayuwa a doron kasa musamman a yankunan da abin ya fi kamari yake burin ina ma shi ne a cikin kabari. Kazantacciyar zubar da jinin da ake yi a yankin Gaza tun daga watan Oktobar bara zuwa yau ya isa abin misali baya ga rikicin da ya zama kamar cin kwan makauniya irin na Somaliya ko Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sannan ga wanda ake fama da shi a tsakanin Rasha da Ukraine. Tambayar da kowa ke yi ita ce, yaushe masu haddasa wannan husuma za su bar al’ummar duniya ta numfasa?
- Kasar Sin Ta Bayyana Damuwa Game Da Halin Da Ake Ciki Tsakanin Iran Da Isra’ila
- Bangaren Kera Motoci Masu Amfani Da Lantarki Na Kasar Sin Ya Yi Kira Ga EU Da Ya Gudanar Da Bincike Bisa Adalci
Mai karatu, na ci karo da wata kwakkwarar amsa a yayin da na samu labarin shawarar da kasar Sin ta gabatar mai taken Yunkurin Tabbatar da Tsaron Duniya, wadda Shugaba Xi Jinping ya ambata a jawabinsa na bude taron Dandalin Boao, ranar 21 ga watan Afrilun 2022.
Wannan shawara cikin hikima da basira tana nuna matsayin kasar Sin na neman samar da ingantaccen tsaro mai amfanarwa tare da wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Kasar Sin ta ba da shawarar kafa sabuwar hanyar tsaro bisa manufar tabbatar da tsaro na bai daya, da zai zama cikakke bisa hadin gwiwa wanda zai dore tare da mutunta juna a matsayin babban ginshiki. Haka nan shawarar tana neman a samar da wani tsari da zai sanya rashin rarraba tsaro a matsayin muhimmiyar ka’ida, da sanya burin samar da al’umma mai cikakkiyar tsaro a gaba.
Karin wani abin sha’awa game da wannan shawarar ta Yunkurin Tabbatar da Tsaron Duniya da kasar Sin ta gabatar shi ne, yadda ta kawo maslaha da tattaunawa da hadin gwiwa a matsayin mafita a maimakon amfani da adawa ko kawance na taron dangi.
Alamu sun nuna wannan shawara za ta samu nasara bisa yadda kasashe fiye da 100 da kungiyoyin yanki da na kasa da kasa suka yi na’am da ita tare da shigar da ita cikin kundayen huldar da ke tsakaninsu da kasar Sin, inda hakan ya sa ta zama abu mai muhimmanci ga sha’anin tsaron duniya.
Wannan tsari da shawarar ta kawo ya sha bamban da irin na kasashen yamma kamar su Amurka da ya jefa mu cikin alkaba’in tashe-tashen hankulan da muke gani a duniya. A tsarin tsaron su Amurka, kansu kawai suka sani ba ruwansu da saura da yi wa abin tanadi na fitar hankali kamar yadda Amurka ta ware Dala biliyan 886 a kasafinta na 2024 a fannin soja kawai. Wannan adadi da ya karu da kimanin Dala biliyan 30 a kan na bara, ba a taba ganin irin sa a tarihin kasar ba.
Har ila yau, sun hana duniya zaman lafiya domin kare muradun kansu ta hanyar kirkiro da kawance na soji daban-daban masu rarraba kawunan kasashe da kakaba takunkumai na karya tattalin arziki da tauye hakkoki da muradun kasashe wadanda dokokin duniya suka halatta da kuma zama kanwa uwar gami na wargaza sha’anin tsaron kasashe kamar yadda muke gani a Palasdinu da Tekun Kudancin Sin da Yankin Koriya.
Wannan ya sa nake da yakinin shawarar tabbatar da tsaron duniya da kasar Sin ta gabatar za ta wanzar da adalcin da ake fatan gani da zai zama silar magance alkaba’in duniya da kawar da tarnakin bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasashe.