Rundunar Sojan Sama ta Operation Delta Safe ta lalata wasu matatun Mai ba bisa ka’ida ba da kuma jiragen ruwa hudu a Jihar Ribas.
NAF, a wata sanarwa da Daraktan Hulda da Jama’a da Yada Labarai (DOPRI) ya fitar, Air Bice Marshal Edward Gabkwet ya ce an kai harin ne tsakanin 12-13 ga Afrilun 2024 a wasu wurare a jihar.
- Jihar Benuwai Ta Bankado Mutum 35 Masu Yi Wa Sirin Tattara Harajinta Zagon-Kasa
- Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Neman Zama Madaukakiya Tare Da Sake Waiwayar Dokokin Kasa Da Kasa
ABM Gabkwet ya ce an kai hari ne da jirage kan barayin mai da ke fasawa da kuma fitar da danyen mai daga bututun ba bisa ka’ida ba.
Mai magana da yawun sojojin ruwan ya ce jirgin a yankin Idama, ya lura da wani wurin gudanar tacewa ta haramtacciyar hanya.
Bugu da kari, wani bincike da aka yi a tsibirin Yellow da tashar Cawthorne ya bayyana wasu jiragen ruwa guda hudu cike da kayan da aka tace mai ba bisa ka’ida ba, suna zuwa Kudu.
Sakamakon haka, jiragen sun shiga hannu kuma aka lalata su.
Gabkwet ya ce an gudanar da bincike makamancin haka a yankunan Ogbomkiri, Arugbana, Iby Island da Samkiri. Ya ce hukumar ta ISR a Ogbomkiri, ta lura da wani wurin tace maia ta haramtacciyar hanya kuma ta aiwatar da hakan. Har ila yau, a Arugbana, an ga barayin mai suna kokarin kafa wani haramtaccen wurin tace mai, kuma da suka ga jirgin da ke gabatowa, sai suka yi kaca-kaca da wurin suka tsre domin tsira da rayukansu.
Hakazalika, an lura da wuraren da haramtattun wurare a SAMKIRI, don haka, an shiga tare da ganin a lalata wurin.
“Baki daya, an gano wuraren da haramtattun wuraraen tace 7 da kuma jiragen ruwa 4 a cikin kwanaki biyu da aka kwashe ana aikin,” in ji shi.