Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi, ya ba da umarnin fitar da Naira miliyan 309.5 domin biyan tallafin Kudaden Karatu ga ‘yan asalin Jihar Kebbi da ke karatu a kasashen Indiya da masar su 86.
Kwamishinan ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar, Alhaji Isah Abubakar Tunga ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi.
- Karancin Wuta: Majalisa Ta Gayyaci Ministan Lantarki
- Dakatar Da Ganduje: Alkalin Ya Yi Watsi Da Umurnin Da Ya Bayar
Ya ce, “Gwamna Nasir Idris ya biya kudin tallafin karatu na kasashen waje ga ‘yan asalin jihar Kebbi da ke karatu a Indiya da Masar har Naira miliyan 228.1 ga dalibai 63 a Indiya da kuma Naira miliyan 81.4 ga dalibai 23 da ke a kasar Masar.
Hakazalika, ya kara da cewa, sauran daliban kasashen waje guda 50 nan ba da jimawa ba za a biya nasu kudaden cikin kankanin lokaci.
Ya kuma kara da cewa, gwamnan ya biya duk daliban jihar da ke karatu a manyan makarantu 36 a fadin Nijeriya tallafin karatu a watan Fabrairu, 2024.