Kocin kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa da ke Ingila, Unai Emery ya sabunta yarjejeniyar zamansa a kungiyar har zuwa shekarar 2027.
Emery, ya karbi ragamar jagorancin kungiyar a watan Nuwamban 2022 lokacin da kungiyar ke matsayin na 17 a teburin Firimiyar Ingila.
- An Kori Sojoji 2 Daga Aiki Kan Aikata Sata A Kamfanin Dangote
- Tinubu Zai Kai Ziyarar Aiki Netherlands Da SaudiyyaÂ
Aston Villa ta yaba da yadda kocin mai shekaru 52 ya sauya kungiyar cikin kankanin lokacin, inda yanzu ta ke a matsayi na hudu a gasar.
Idan kungiyar ta karkare a matsayin da ta ke, hakan zai ba ta damar buga gasar zakarun Turai a kaka mai zuwa.
Unai Emery, ya horas da kungiyoyi irin su Sevilla, Villarreal, Arsenal, PSG da sauransu kafin zama kocin Aston Villa.