Wasu Malaman addinin Kirista da suka fito daga Arewacin Nijeriya sun kai wa Sarkin Kano na 14 kuma Khalifan Tijjaniyya a Nijeriya, Sanusi Lamido Sanusi ziyarar ban girma a gidansa da ke jihar Kaduna.
Malaman sun kai ziyarar ce da nufin kara karfafa wanzar da zaman lafiya a tsakanin mabiya addinin Musulunci da na Kirista.
- Sanusi Ga ‘Yan Nijeriya: Ku Dora Wa Buhari Alhakin Matsatsin Tattalin Arziki Ba Tinubu Ba
- Yadda CBN Ya Karya Darajar Naira – Sanusi
Babban Limanin Cocin Christ Ebangelical and Life Interbention Ministry da ke a Jihar Kaduna, Dakta Yohanna Buru ne ya jagoranci tawagar. Haka zalika, sun kai ziyarar ce domin jaddada muhimmancin martaba addinan juna da kara hadin kai a tsakanin mabiya addinai.
A jawabinsa, Buru ya jinjina wa Khalifa musamman a kan irin gudunmawar da yake ci gaba da bayarwa na wanzar da zaman lafiya don ci gaban kasar nan.
A cewar sa, Khalifa ya jima yana dabbaka wanzar da zaman lafiya da yada girmama addinan biyu da shigewa kan gaba wajen tattanawa ko yin muhara a kan zaman lafiya ba a Nijeriya kawai ba, har ma a daukacin fadin Nahiyar Afirka.
Tawagar ta kuma yaba masa a kan namijin kokarin da yake ci gaba da yi, na yada zaman lafiya, mussamman kan gudunmawar da ya bayar na lalubo da mafita kan takaddamar kungiyar ECOWAS biyo bayan kifar da gwamnatin farar hula da sojin jamhuriyar Nijar suka yi a watannin baya, wanda suka yi nuni da cewa, wannan kokarin nasa ya cancanci a karrama shi da babbar lambar yabo ta duniya ta wanzar da zaman lafiya.
Shi ma a nasa jawabin Fasto Alhamdu John wanda ya zo daga Babban Birnin Tarayya Abuja ya bayyana jin dadinsa bisa samun ganawa da Khalifa Sanusi, inda ya kara da cewa, manufar ziyarar ita ce don a kara karfafa dankon zmunci da hadin kai.
Shi kuwa Fasto George Joshua daga jihar Biniwe, da yake yin tsokaci a kan gudunmawar da Khalifa ke ci gaba da bayarwa a matsayinsa na mabiyin darikar sugaye ta Tijanniyah, ya jaddada mahimmancin ganin mabiya Musulunci da Kirista na yin aiki da koyar da addinansu domin ci gaba da wanzar da zaman lafiya, kauna da kuma hadin kai.
A nasa bangaren, Khalifa Sanusi Lamido ya bayyana jin dadinsa bisa wannan ziyarar tare da yaba wa malaman addinin a kan tasu gudunmwar da wajen wanzar da zaman lafiya, musamman a Arewacin kasar nan.
Khalifa ya yi nuni da cewa, wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma aiki ne da ya rataya a kan kowanne dan kasa.