An bude taron karawa juna sani kan bukasa kimiyyar karatu daga nesa a babban dakin taro na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (Assembly hall).
Manyan mutane sun gabatar da mukaloli da dama da suke kira akan bunkasa harkar kimiyyar karatu daga nesa tare da kawo amfaninsa ga al’ummar kasa da kuma magance kalubalen da ke cikinsa.
Daga cikin manyan bakin da suka sami halartar wannan taro akwai wakilin babban sakataren Hukumar Kula da Jami’o’I ta Kasa, Mista Chris J. Mai Yaki, da wakilin Mataimakin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Farfesa Ahmed Dako Ibrahim da Hajiya Rakiya Gambo Iliyasu, darakta daga U.E.F da sauran manyan baki daga kasashen ketare
Bayan kammala bude taron ne, shugaban kwamitin taron kuma shugan tsangayar karatu daga nesa (Distance Learning) na Ahmad Bello Zaria Farfesa Ibrahim Sule ya yi wa manema labarai karin haske kamar taron wanda ya bayyana cewa idan ‘Yan Nijeriya suka rungumi tsarin, za a samu karin mutane da suka halarci manyan makarantu a Nijeriya.