‘Yan Bindiga sun harbe wani yaro dan shekara bakwai mai suna Ayuba a yankin Paikon Basa a anguwar Gurdi dake Abaji, Abuja.Â
Wani mazaunin garin, James Gwatana ne ya sanar da cewa, ‘yan Bindigar sun shiga yankin dauke da bindigu a daren juma’ar da ta gabata, suna ta harbe-harbe, hakan ya janyo mutuwar yaron.
Ya ce, ‘yan Bindigar sun kuma yi awon Gaba da wasu kayayyakin masarufi a wasu shaguna a yankin tare da yin garkuwa da mutane 10.
Dagacin yankin Gulida, Abubakar Sardauna, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce hudu daga cikin mutanen da aka sace sun arce daga sansanin ‘yan Bindigar.
An rahoto cewa, bayan harin, ‘yan Bindigar sun kuma afkwa yankunan Mawogi, inda suka yi garkuwa da mutane shida.
Rundunar ‘yan sanda ta Abuja har yanzun ba ta ce uffan ba kan kai harin na ‘yan Bindigar na yankin ba.