A halin yanzu Attajirin nan Alhaji Rabiu Abdulsamad da dansa sun samu ribar fiye da dala miliyan 79.4 daga hakokin kasuwancinsu na kamfaninsu na samar da abinci, ana sa ran kudin zai shiga asusun a jiyarsu ta banki ne daga nan zuwa ranar 26 ga watan Satumba na shekaar 2024 bayan an samu amincewar babban taron kamfanin na shekara-shekara.
Bincike ya tabbatar da cewa, Abdul Samad Rabiu, wanda shi ne mutum na uku cikin masu kudin Nijeriya zai karbi kudadaen ne daga cikin ribar hannun jarinsa a kamfanin samar da kayayyakin abinci na ‘BUA Foods Plc’. Kamfanin da ke a kan gaba wajen samar da kayayyakin abinci daban-daban a Nijeriya dama yankin Afirka gaba daya. Wannan ribar da za a bashi kuma yana da cikin kudaden da kamfanin ta samu ne a shekarar 2023 wanda ya kai naira biliyan 206.32 wanda ya yi daidai da dala miliyan 166.41.
- Fara Aikin Matatar Dangote Da Ta Fatakwal: Jama’a Na Dokin Karyewar Farashin Fetur
- Shugabannin Sin Da Tanzaniya Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 60 Da Kafuwar Huldar Diplomasiyyar Kasashen Su
Kamfanin ‘BUA Foods’ na daga cikin manya-manyan kamfanoni da ke karkashin uwar kamfanin BUA wanda suke yi sigari, man gyada da flawa da kuma taliya da macaroni har ma da shinkafa. Abdul Samad Rabiu da dansa Isyaku Naziru Rabiu, nada hannun jarin da ya kai kashi 99.8 a kamfanin gaba daya.
Dala miliyan 79.4 da za a raba musu zai tafi ne kai tsaye zuwa asusun ajiyarsu na banki bayan hukumar gudanarwa kamfanin sun amince da yadda za a rarraba ribar ga sauran masu hannun jari.
Wannan ne karo na uku da kamfanin ke samun karin riba a cikin ‘yan shekarun nan, duk kuwa da karayar tattalin arziki da duniya ta fuskanta. Wannan na nuna irin yadda kamfanonin abinci ke samun bunkasa a yanayin tabarbarewar tattalin arzikin kasa.