Yayin da ya rage saura kasa da kwanaki 10 a fara jigilar Alhazai zuwa kasar Saudiyya daga dukkan kasashen Musulmin duniya, wata kungiya mai zaman kanta da ke sa ido da kuma bayar da rahoto kan harkokin aikin hajji (IHR), ta yi kira ga Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) da ta sanar da ranar da za a fara jigilar maniyyatan Nijeriya zuwa Saudiyya.
IHR ta ce, kusan dukkan manyan kasashen da ke halartar aikin Hajji sun sanar da ranar da za su fara jigilar maniyyata daga kasashensu. Don haka, ya zama al’ada a kasar nan, NAHCON, ta sanar da ranar da wuri.
Kungiyar ta ce, kawo yanzu manyan kasashe 5 na duniya da suka fi yawan alhazai sun bayyana lokacin da za su fara jigilar alhazansu.
“Alhazan Nijeriya dai, sun hada da ma’aikatan gwamnati, manoma, ‘yan kasuwa da mata. Ana sa ran kowane mahajjaci zai shafe kwanaki 28 zuwa 30 a kasar Saudiyya, don haka, suna bukatar bayanai kan lokacin tafiyarsu don samar da isasshen abinci ga iyalansu da wadanda suka dogara da su.
Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta kasa, bata bayyanawa maniyyata kudin tallafinsu na tafiya ba (BTA).