Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da Real Madrid sun tashi 2 da 2 a wasan gasar zakarun turai (Champions League) da suka buga a filin wasa na Allianz Arena.
Munich ta karbi bakunci Madrid ne a daren ranar Talata, a wasan kusa da na karshe na gasar.
- Yan Sama Jannatin Shenzhou-17 Sun Dawo Doron Duniya
- Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Kara Wa Ma’aikata Albashi
Dan wasan gaban Real Madrid, Vinicius Junior ne ya fara jefa kwallo a minti ma 24 da fara wasan.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Bayern ta farke kwallon ta hannun dan wasanta Sane, sannan ta kara kwallo ta hannun Harry Kane a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
A minti na 83 Vinicius Junior ya warware kwallon da Munich a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Kungiyoyin biyu za su sake karawa a ranar Laraba a mako mai zuwa a gidan Real Madrid.