Daruruwan kauyuka a sassa daban-daban na Nijeriya ne suka tsinci kansu a rashin samun damarmakin bunkasa tattalin arziki, kiwon lafiya da kuma ilimi sakamakon rashin hanyoyi da za su yi zirga-zirga a kansu da kuma yadda hanyoyin ruwa suka zama tarkunan mutuwa wajen yin sufuri da zuwa gonaki.
Ko da yake babu kididdiga a hukumance ta adadin mutanen da suka mutu a sakamakon hatsarin jiragen ruwa ko kwale-kwale, sai dai a wani binciken da LEADERSHIP ta gudanar, ta gano cewa daruruwan rayuka ne aka rasa a shekarar da ta gabata sakamakon rashin bin ka’ida da dokoki da kuma rashin zuba hannun jari yadda ya dace a sha’anin sufurin jiragen ruwa.
- NAHCON Ta Ayyana 15 Ga Watan Mayu Ranar Tashin Alhazan Farko Daga Nijeriya
- An Gurfanar Da Mutane 2 A Kotun Sojoji Kan Harin Tudun Biri
Wani babban abun da ke kara toshe al’ummomin daga samun ababen more rayuwa shi ne, rashin tabuka wani abun a zo a gani daga gwamnatoci ta hanyar gina musu gadoji da zai hada wannan al’ummar da wancan.
A cewar wasu daga cikin masu ruwa da tsaki, wani bari daga cikin matsalar shi ne, yadda mutanen da ba su da aikin yi rana guda kan wayi gari kawai su shiga harkar jigilar mutane da kayayyaki ta hanyoyin ruwa domin samun kudi.
Shugaban kungiyar masu kera jiragen ruwa (MCBA), Clem Ifezue, ya ce ana ci gaba da ganin ibtila’o’I a magudanan ruwa sakamakon yadda hukumar kula da hanyoyin ruwa ta Nijeriya (NIWA) ba ta yin abun da ya dace wajen tsaftace hada-hadar hanyoyin ruwa da suke fadin kasar nan.
Ifezue ya ce, “Dukkaninmu mun ji cewa marigayiyar tauraruwar masana’antar shirya fina-finan na kudanci (Nollywood) ta ki sanya rigar kariya kuma a haka aka bar ta ta shiga cikin jirgin ruwa aka ja ta. Shi ya sa suka rasa rayukansu.
“Irin wannan da daman gaske suna faruwa, muddin in ba za a mu bi dokoki da ka’idoji ba dole a ci gaba da samun akasi. Zaman tattaunawa a tsakanin masu tabbatar da bin ka’ida, masu gudanarwar da jiragen ruwa da masu kaya da masu lodi na da matukar muhimmanci a wannan lokacin.
“Don haka, abubuwa da dama ke janyo hatsarin jiragen ruwa, daya daga cikinsu shi ne, tukin ganganci daga wajen matuka jirgin. Mun ba da shawarar cewa dukkanin wani nau’in giya ko kayan maye da ka iya sanya mutum maye a haramta sayar da su a kusa da masu tukin jiragen ruwa. Dalili shi ne, wadannan matuka za su amsa su sha, domin su samu kuzarin jikinsu, sannan da zarar direba ya fara wani irin tuki na fita hayyaci zai je ne ya kashe mutane kawai.” Ya bayyana
Alal misali a Jihar Imo, ‘yan kasuwa masu zaman kansu ne kawai ke yin jigilar mutane ta hanyoyin ruwa, inda al’umman kauyuka ke amfani da wannan damar wajen tashi daga Amaraocha da ke Oguta zuwa gonakansu da sauran wurare domin rage cin lokaci.
Jami’in watsa labarai na jam’iyyar APC a Oguta, Hon Adigwe Ossai, ya yi bayanin cewa gonakai da daman gaske da suke Oguta suna wuraren da ke da tazarar sama da kilomita 15 ne daga kauyukan, don haka jama’a na amfani da hanyoyin ruwa wajen ratsawa zuwa gonakinsu.
A cewarsa, mutane da dama kan shiga cikin babban jirgin ruwa da motocinsu da zai dauke su zuwa inda suke so, kana babban jirgin na daukan motoci sama da goma har ma da manyan motoci.
Ossai ya ce masu yawon bude ido da dama a ranakun Lahadi kan shiga cikin jiragen ruwa masu saurin gudu sanye da rigunan kariya.
Sai dai duk da hakan ya ce an taba samun hatsarin jirgin ruwa shekaru uku da suka wuce lokacin da wata babbar mota dauke da siminti ta rufta a cikin kogi.
Adadin wadanda hatsarin jiragen ruwa ya shafa ya fi kamari a jihar Ribas. Adadin mutum 14 ciki har da yara biyar ne suka rasa rayukansu a hatsarin jiragen ruwa biyu da suka wakana a shekarar da ta gabata.
A ranar 9 ga watan Janairun 2024, fasinjoji mutum 11 ciki har da yara biyar da suka fito daga zuri’a guda ne suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin ruwa da ya wakana a hanyar ruwan Andoni zuwa Bonny a karamar hukumar Andoni da ke jihar.
Hatsarin ya faru ne a lokacin da wani jirgin kamun kifi da ya kwaso masunta da fasinjoji sama da 100 daga yankin Ngo, shalkwatar karamar hukumar Andoni zuwa Bonny, ya yi taho-mu-gama da wani jirgin ruwa na fasinjoji da shi kuma ke tahowa ta wata hanya ta daban.
A ranar 8 ga watan Afrilun 2024, fasinjoji mutum uku dukkaninsu mata ne suka mutu a lokacin da jirgin ruwa mai kwaso fasinjoji ya yi hatsari a kogin Bonny da ke karamar hukumar Bonny a jihar.
An gano cewa, fasinjoji 11 ne suke cikin jirgin kuma an ceto su illa uku daga cikinsu likita ya tabbatar da mutuwarsu.
Da yake bayani kan abubuwan da ya gani, wani da ya tsalleke siradi a hatsarin jirgin ruwa, Fasto Promise Festus, ya ce ya rasa ‘ya’yansa hudu da kuma kakansa a hatsarin jirgin ruwa da ya wakana a ranar 9 ga watan Janairun 2024, a kan hanyar ruwa da ya taso daga Andoni zuwa Bonny.
Festus, wanda mamallaki kuma matukin wani jirgin ruwa na kamun kifi ne, ya yi bayanin cewa hatsarin ya faru ne a kusa da LGN Jetty, a lokacin da suke hanyarsu ta dawowa daga yankin Ngo zuwa Bonny Island bayan kammala bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Ya ce ya kwashi ‘yan mutane kalilan wajen yin tafiyar saboda ba su da kudin da za su biya zuwa Bonny.
“Na je domin yin bikin Kirsimeti tare da iyalaina. A lokacin da muke hanyar dawowa, a ranar 8 ga watan Janairu na kwaso mutane wadanda ba su da kudin da za su iya biya na jigila tare da iyalaina. Bisa tsautsayi, kwale-kwalenmu ya yi hatsari a gaban LNG, amma ba a samu aka ceto su ba. Don haka kusan mutum sha daya suka mutu kuma biyar daga ciki ‘ya’ya ne.”
A Jihar Benuwai, kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Catherine Anene, ta ce daga 2023 zuwa yanzu, hatsarin jirgin ruwa guda daya kawai aka samu da ya janyo mutuwar mutu daya tak.
Kazalika, wani matukin jirgin ruwa daga yankin Wadata ta Jihar Beniwai ya ce daga shekarar 2023 zuwa yanzu babu wani direban jirgin ruwa da ya mutu a yayin da yake bakin sana’arsa a yankin.
Matukin jirgin ruwan wanda ba ya son a bayyana sunansa ya bukaci gwamnati ta wadata cibiyoyin da ke jigilar fasinjoji ta jiragen ruwa da rigunan kariya domin kare rayukansu idan hatsari ya wakana.
Ya ce, wasu daga cikin hatsarin jiragen ruwa sun faru ne sakamakon rashin kwarewar wasu daga matuka jiragen da ke tsunduma cikin sana’ar kawai don sun rasa abun yi.
“Ina rokon gwamnati da ta horas da wasu daga cikin matuka jiragen ruwan kan matakan kariya da kiyayewa a yayin da suke cikin ruwa domin ganin an rage yawaitar aukuwar hatsarin jiragen ruwa.”
Har ila yau, a watan Yunin shekarar da ta gabata, sama da mutum shida ne suka mutu a kogin Ughoton da ke kusa da kauyen Jeddo a karamar hukumar Okpe ta Jihar Delta, lokacin da jirgi mai gudun tsiya da ya kwaso fasinjoji tara ya gamu da hatsari, bayan da ya bugi wani abu mai kauri a cikin kogin.
Fasinjojin da tsautsayin ya rutsa da su sun fito ne daga bikin bizine wani mamaci a kauyen da ke makwaftaka da su.
A cewar majiyoyi daga yankin, hatsarin ya faru ne cikin dare don haka lamarin ya kasance mai matukar wuya ga mutane su iya ceto su. Amma mutum uku sun kubuta.
Daya daga cikin wadanda suka tsira a hatsarin, Bright Oshuko ya ce, “Taimakon Allah ne kawai ya cece mu kuma an ci sa’a na iya iyo a cikin ruwa. Mu tara ne a cikin jirgin, uku daga cikinmu ne kawai suka iya yin iyo domin neman tsira a cikin daren.
“Lamarin ya yi kamari sosai sakamakon cikin dare ne hatsarin ya faru. Na yi ta kokari na samu na yi iyo zuwa wata bishiya, inda na makale kaina a wajen har zuwa safiya. Wurin ya yi matukar duhu da wuya ka ga abin da ke gabanka ko ka ji motsin wani abu. A zuciyata, ina fargabar zan iya cin karo da kifaye, macizai da sauran dabbobin ruwa. Abun da ya fi a’ala kawai shi ne mutum ya makale kansa a wani wajen.”
Gwamnatin Jihar Delta ta haramta yin tuki ko shiga cikin ruwa domin yin tafiye-tafiye ba tare da sanya rigar kariya ba, saboda shirin ko-ta-kwana a wani mataki na kariya.
Kwamishinan yawon bude ido da al’adu na jihar, Dakta Nnamdi Ijeh ya bayyana haka a yayin da yake tsokaci kan hatsarin jiragen ruwan da suka wakana a jihar, musamman wanda ya janyo mutuwar wasu mutane a cikin jirgin a kogin Neja a makonnin da suka wuce.
Ya ce dole ne ake bin matakan kariya, ita kuma gwamnati a bangarenta za ta tabbatar matuka da fasinjoji na bin ka’ida, a kuma matakinta na kiyaye faruwar hakan gaba da rage yawan tafiye-tafiya ta jiragen ruwa, ya ce gwamnati za ta gina gadaje domin bai wa mutane damar ratsa garuruwa.
Shi kuma wani ma’aikacin jirgin ruwa, Simon Ekpa ya ce masu jigilar fasinjoji a hanyoyin ruwa ba su da wata takamaimamiyar tasha ko wurin da suke fakin don haka, da wuya ake bin matakan kariya da suke dauka kana ga nuna sakaci daga wajensu.
Ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta bar jihohi da kananan hukumomi su kula da hanyoyin ruwa, walau koguna ne ko kuma teku ta yadda za a iya samun damar bibiya da tabbatar da masu jiragen ruwa na bin dokoki da ka’idoji.
“Ko mai kiwon kifi ma ya tsunduma jigilar fasinja a cikin ruwa. Wadanda suka ce suke da alhakin hanyoyin ruwa ba su a kogunan balle su san mene ne ke faruwa a wajen. Akwai abubuwa da dama da suke faruwa a sha’anin jigilar ruwa da suke bukatar a dauki matakan kula da su. Shin ko kun san akwai wasu da suke tuka jiragen ruwa cikin dare ba tare da wuta ba?
Wani hatsarin jirgin ruwa da ya wakana bisa lodin ganganci da tukin ganganci, shi ne wanda ya faru a ranar Alhamis 6 ga watan Afrilun 2023, lokacin da wani jirgin ruwa MB Tari da ya kwaso fasinjoji 95 dauke da kayansu daga Yenagoa ta Jihar Bayelsa zuwa Okpoama da ke karamar hukumar Brass, inda jirgin ya yi hatsari a kusa da Iwokiri a Okoroma.
Jirgin wanda aka ce ya tsaya wajajen karfe 8:45 na safiya a Okodi Obia, Dogioma, Akakimama da kauyen Olokiama domin kara kwasar fasinjoji kafin daga bisani hatsarin ya faru da karfe 2:35 na rana a kwanar Brass, ya kashe mutum takwas ciki har da yara.
Ganau sun ce matukin jirgin ruwan a lokacin da ya je wani waje ya tarar da ruwan hanyar ya shanye kuma ba shi da zurfi nan take ya yi kokarin juyawa, amma sakamakon tsula gudun tsiya da yake yi nan take ya kife. Durom-durom na man fetur da sauran kayan da ke cikin jirgin sun kama da wuta a cikin ruwa tare da fasinjoji, lamarin da ya janyo kifewar jirgin daga bisani.
Kazalika, a ranar Laraba, 25 ga watan Oktoba, 2023, an bayyana cewa wani dan jarida a Bayelsa, Mista Perry Tukuwei Jr, ya bace daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa a hatsarin jirgin ruwa a lokacin da shi da wasu ‘yan jarida suke tafiya daga Nembe zuwa kauyen Okoroba a karamar hukumar Nembe domin yakin neman zaben dan takarar gwamnan APC.
Wani da ya kubuta daga hatsarin wanda tsohon shugaban sashin kula da labarai na AIT reshen Yenagoa ne, Mista Abwarosub Jonathan Juri, ya ce tabbas hatsarin ya faru ne sakamakon ganganci da gudun tsiya da matukin yake yi.
Kan hakan ne ya shawarci jama’a da a kowani lokaci su rika amfani rigar ruwa da zarar sun shiga cikin jirgin ruwa ko kwale-kwale domin yin tafiya a cikin kogi ko teku.
Ya kara da cewa, akwai bukatar tsaurara doka kan matuka jirgin ruwan domin ganin suna bin ka’idojin tuki.