Hedikwatar tsaro ta kasa, ta dauki alhakin harin da jiragen yaki suka kai Tudun Biri da ke Jihar Kaduna, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a watan Disamban 2023.
Daraktan tsaro na rundunar, Manjo Janar Edward Buba ne, ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi a ranar Alhamis.
- Nijeriya Da Japan Sun Kulla Yarjejeniya Don Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Yankin Sahel
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda, Sun Ceto Mutane A Katsina Da Filato
Ya ce rundunar ta kammala bincike kuma ta dauki alhakin kai harin kan kuskuren wadanda ya kamata ta kai wa harin tun da fari.
LEADERSHIP ta ruwaito yadda harin na ranar 3 ga watan Disamban 2023, ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 88 a Tudun Biri.
Buba ya ce wadanda ke da hannu a kai harin za a gurfanar da su a kotun soji don fuskantar hukunci.