Babban Sakataren Ma’aikatar Kasuwanci da Zuba Jari ta Tarayya, Nura Abba Rimi; ya bukaci masu ruwa da tsaki a fannin noman Kwakawar Manja, su yi amfani da fasahar zamani da kere-kere, don samar da girbi mai yawa tare da kokarin rage yin asara da kuma kara habaka fannin.
Rimi ya bayyana hakan ne, a wata ganawa da ya yi da masu ruwa da tsaki a fannin a garin Benin na Jihar Edo.
- Gwamnatin Tarayya Ta Jaddada Aniyar Karfafa Wa Mata Shiga Harkar Ma’adanai
- Kotu Ta Hana ‘Yansanda Kama Shugabannin Jam’iyyar APC Da Suka Dakatar Da Ganduje A Kano
Har ila yau, ya kuma shawarce su da su rungumi amfani da dabarun kula da Bishiyoyin Kwakwar Manjan, musamman a gonakin da aka shuka su.
Wani jami’in a sashen kasuwanci na ma’aikatar, Gambo Garba Magaji; shi ne ya wakilici Babban Sakataren a wajen ganawar.
Kazalika, Rimi ya bukaci masu ruwa da tsakin; su yi duba a kan kalubalen da ke gabansu tare da yin aiki kafada da kafada, don tabbatar da ganin wannan fanni ya samu nasarar da ake bukata.
Jihohi shida ne suka halarci wannan ganawa, wadda sashen kasuwanci da fitar da kaya zuwa kasashen ketare na ma’aikatar ta kasuwanci da zuba jari ta tarayya ta shirya tare da hadaka da kungiyar masu samar da Kwakwar Manja ta kasa (NPPAN).
Wadannan jihohi sun hada da Kuros Ribas, Akwa Ibom, Abiya, Imo, Edo da kuma Ondo.
Haka zalika, Rimi ya ce, “Dole ne mu yi duba a kan muhimmancin yin hadaka da ilimi, don habaka inganata hadakar ta hanyar yin amfani da hukumomin da ke gudanar da bincike da yin amfani da kwararrun da suke a masana’antu tare da yin amfani da hukumomin kasa da kasa”.
A cewarsa, ta hakan ne za mu samu irin kwarewar da suke da ita, musamman don kara habaka wannan noma na Kwakwar Manja a fadin wannan kasa baki-daya.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban kungiyar Alphonsus Iyang, ya shawarci gwamnatin tarayya ta kirkiro da wuraren sarrafa Kwakwar Manja a daukacin jihohin da ke noma Kwakwar Manjan.
Ya ce, kirkiro da wadannan wurare ko shakka babu; zai taimaka wa kananan manoma da ke aiwatar da wannan noma na Kwakwar manja.
Shi kuwa Kwamishinan Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Abinci na Jihar, Stebe Ideheenre; kira ya yi da a mara wa masu ruwa da tsaki baya a wannan fanni.