Jarumar fina-finan Hausa na Kannywood Fati Layo Dorayi wadda aka fi sani da Kyauta Dillaliya, a wata hira da ta yi da manema labarai ta bayyana abubuwa da dama da suke faruwa a masana’antar ta Kannywood inda ta bayyana cewar ba za ta iya bari ‘ya’yanta su shiga harkar fim a nan gaba ba.
Ba komai ne ya sa nake tsoron ‘ya’yana su shiga harkar fim ba illa tsinuwar da ake yi wa jaruman fim ana kiransu da ‘yan iska ko kuma mutanen banza duk wata harka da za su shiga idan har za ta kawo alheri zan iya barinsu su shiga amma banda harkar fim saboda mafi yawan mutane suna tsine wa jaruman Kannywood suna yi masu kallon wadansu tsinannu ko kuma ‘yan iska in ji ta.
- Sauya Sheka: Jam’iyyu Na Shirin Tilasta Kafa Dokoki Masu Zafi A Kan ‘Yan Majalisa
- Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida: AMDF Ta Nemi A Bai Wa ‘Yan Jarida Kariya A Afirka
Dillaliya kamar yadda ake kiranta ta kara da cewar tana takaici idan taga tsala tsalan ‘yan mata kyawawa suna shiga harkar fim da sauran kuruciyarsu a maimakon su je su yi aure su zauna a dakunan mazajensu, domin kuwa duk wadda ta shiga harkar fim alhali tanada sauran kyawunta da kuruciyarta tamkar ta bata rayuwarta ne saboda a wannan lokacin aurene ya kamace ta ba shiga harkar fim ba.
Daga karshe Fatima wadda yanzu haka take takarar zama kansila a gundumar Dorayi da ke Jihar Kano ta bayyana cewar duk wanda zai fada maka cewa gyaran tarbiyya kokuma wa’azantarwa ake yi a Kannywood ya fada maka karya, domin ko kusa babu wani wa’azi ko gyaran tarbiyya da ake yi a Kannywood.