Hukumar tattara kudaden haraji ta jihar Kaduna (KADIRS) ta rufe turakun sadarwa bakwai mallakin kamfanin MTN da Globacom a fadin birnin jihar kan kin biyan kudin haraji da ya kai kimanin Naira Biliyan 5.8.
Shugaban bangaren hulda da jama’a na Hukumar KADIRS, Zakari Muhammad, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
- NNPCL Ya Bayyana Ranar Da Matatar Man Fetur Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki
- Masu Zargin Uba Sani Kan Bashin el-Rufa’i Sun Jahilci Aikin Majalisa – Barista Bello
An kulle turakun ne saboda sabon tsarin tattara haraji da hukumar tsara birane da raya birane ta jihar Kaduna ta kafa (KASUPDA).
Turakun sadarwar da aka rufe sun hada da turakar MTN da ke Tafawa Balewa Way a Unguwan Rimi; turakar GLO da ke titin Shehu Laminu, Unguwan Rimi, da kuma turakar MTN da ke Surami Road, Unguwan Rimi.
Sauran sun hada da turakar MTN da ke Etsu Road, Unguwan Rimi, turakar MTN, Airtel, Glo, 9-Mobile a Nagwamatse Road a unguwar Rimi.