Mataimakin shugaban jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, MAU, Farfesa Abdullahi Liman Tukur mai barin gado, ya bayyana rahoton nasarori, sauye-sauye da ci gaban da ya kawo lokacin da ya shugabanci jami’ar na tsawon shekaru 5.
Shugaban jami’ar wanda ke ganawa da manema labarai a Yola, ya ce, duk da kalubalen da ya fuskanta a lokacin shugabancinsa, kama daga Annobar COVID-19, yajin aikin kungiyar malamai da ma’aikatan jami’o’i da tsadar rayuwa amma makarantar ta cimma nasarori masu dimbin yawa.
- ‘Yan Kasuwa Fiye Da Dubu 221 Daga Ketare Sun Halarci Canton Fair Karo Na 135
- NAHCON Ta Ayyana 15 Ga Watan Mayu Ranar Tashin Alhazan Farko Daga Nijeriya
“Babbar nasarar da na samu a matsayina na mataimakin shugaban wannan jami’a, ita ce, mayar da jami’ar daga babbar jami’a zuwa wata jami’a ta zamani, hakan ya sa jami’ar MAU ta samu daukaka daga durkushewar da ta afka mata a baya.
“Don haka, ban yi da-na-sanin daukar nauyin mayar da jami’ar zuwa yadda take a yau ba.
“Manufarmu, jami’ar MAU ta zama jami’ar kimiyya da fasaha ta duniya ta hanyar kwarewa a fannin koyarwa, koyo da bincike, don haka, dole ne duk masu ruwa da tsaki a wannan bangaren su sake duba wannan kuduri domin tunkarar kalubalen da ke tasowa.
“Babu wata shakka, kokarinmu wata niyya ce ta hada kan al’ummar jami’ar a kan kyakkyawar manufa da tabbatar da cewa jami’ar ta mai da hankali kan sabon canji na zamani da fasaha ke takawa a fannin ilimi da bincike.
“Na karbi ragamar tafiyar da harkokin jami’ar ne a watan Yunin 2019, bayan shekaru uku da cire dukkan fannonin ilimi da aka yi a Makarantar saboda tsarin (SMIT) na wancan lokacin, wanda hakan ya rage yawan adadin sabbin daliban da ke shiga jami’ar.
“Don tabbatar da cewa jami’ar ba kawai ta tsira ba, har ma ta kasance mai dacewa da kalubalen gida da na yanki kamar yadda aka gano a cikin sanarwar hangen nesa na manufofinmu, cikin dabaru da tsari mun fara wani sabon salo wanda ya yi nasarar sauya jami’ar.” Inji Farfesa Liman.