Gabatarwa
A cewar Hukumar Kula da Ilimi da Kimiyya da Al’adu ta Majalisar dinkin Duniya (UNESCO), “Rikicewar yanayi da rabe-raben halittu ba wai kawai ya shafi muhalli da halittu ba ne har ma da rayuwar biliyoyin mutane a duniya. Labarunsu na tashin hankali da hasarar da suka yi ya cancanci zama sanannen al’amari da za a rika ya dawa domin a koyaushe suna iya zama masu tayar da hankali.
Babu lokacin da ya fi dacewa da kafofin yada labarai su tashi tsaye domin yadawa da fadakarwa kamar yanzu, lokacin da babban kalubalenmu shi lalatacewar muhalli.
Kalubalen Rashin Daidaita Bayani Da Rashin Ingantattun Bayanai
Wurin zamanmu na fuskantar barazana daga abubuwa biyu na dan’Adam da na sauran halittu, kuma wadannan barazanar suna kara zama masu hatsari yayin da lamarin ke haifar da mummunan tasiri ga abinci, tsari, da kwanciyar hankali.
Gaggawar yaduwar lamarin na barazana ga yanayinmu, bambancin halittu da kuma kyautata rayuwar al’ummomin dan’Adam. Wadannan batutuwa su ne manyan matsaloli saboda da girmansu, tsananinsa da Tasirinsu na dogon lokaci.
Lalacewar Muhalli A Shiyyar Arewa Maso Yamma
Tun daga yanayin zafi a Gabas zuwa bushewar yanayi A Arewa, dukkanin sassan Nijeriya na nuna lokuta dabandaban na matsalolin muhalli don haka yana bukatar tsarin gudanarwa dabandaban.
Yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya wanda shi ne babban abin da wannan labarin ya mayar da hankali a kai yana fuskantar babban kalubale da rikicewar da ke faruwa a yankin daga zaizaya, guguwa, kwararowar hamada, iska, gurbacewar yanayi, fari, ambaliya, rashin sarrafa shara, gurbacewar hamada, zaftarewar kasa, da kuma kasancewarsa birni da za a ambata nan gaba kadan.
Daga ranar 28 ga Oktoba, 2023, zuwa 25 ga Afrilu, 2024, wani bincike da Cibiyar Kula da Matsugunan Jama’a (IDMC) ta gudanar ya nuna cewa, daga cikin mutum 13,551 da suka rasa matsugunansu a yankin Arewa maso Yamma, 3,758 sun rasa matsugunansu ne sakamakon hadura da ambaliyar ruwa.
Martanin Masu Ruwa Da Tsaki
Babban Daraktan Hadin Gwiwa na ci gaban ci gaban zamantakewa da muhalli (PSEDI), Eme Okang, ta yi karin haske kan kalubalen da ke tattare da muhalli a shiyyar Arewa maso yammacin Nijeriya, da suka hada da kwararowar hamada, sare itatuwa, gurbacewar kasa, karancin ruwa, zaizayar kasa, da kuma lalatacewa kasa.
Wadannan batutuwa na da matukar tasiri ga al’ummomin yankin, wanda hakan ke haifar da rashin kwanciyar hankali game da tattalin arziki da matsalolin kiwon lafiya. Okang ta jaddada rawar da rahoton bincike da bayar da shawarwari kan aikin jarida ke bayarwa wajen wayar da kan jama’a da kuma daukar matakai kan al’amuran muhalli.
Ta zayyana muhimman hanyoyi guda biyar da za a bi domin cimma wannan hadin gwiwa, inda ta jaddada shiryeshiryen gwamnati, hulda da jama’a, kwarewar kungiyoyin sa-kai, hadin gwiwar jama’a da masu zaman kansu, da kuma rawar da kafofin yada labarai ke takawa a matsayin abin dogaro.
Jihohin Kebbi, Kano, Jigawa, Zamfara, Sokoto, Katsina, da kuma Kaduna wadanda ke Arewa maso Yammacin Nijeriya na fama da matsalar karancin muhalli da hakan ke kara kamari a Nijeriya.
Abin takaicin shi ne, da yawa daga cikin rashin isassun bayanai da rashin ingantattun bayanai sun mamaye wannan batu saboda yada jita-jita da labaran karya, hasashe, rashin ingantaccen aikin jarida da rashin manufofin gwamnati game da wannan batu.
Irin wadannan al’amura da suke barazana ga rayuwa da lalata muhalli suna bukatar kulawa sosai da da wayar da kai. Duk da haka, akasin haka shi ne aka fi cin karo da shi yawan lokuta.
Babban Jami’in Kula da Lafiyar Muhalli a Jami’ar Tarayya Dutsin-Ma ta Jihar Katsina, Muktar Mustapha, ya bayyana matsalolin da ke addabar al’umma da dama a Jihohin Arewa maso Yamma, musamman Jihar Katsina, wadanda suka hada da sare itatuwa da lalata muhalli da ke barazana ga namun daji.
Yankin kuma yana fama da hauhawar yanayin zafi da yanayi mara kyau, wanda ke yin illa ga ayyukan noma da rayuwar yau da kullum. Ayyukan hakar ma’adanai a kananan hukumomin kamar Kankara, Batsari da DanMusa suna taimakawa wajen lalata kasa, zaizayar kasa, da ambaliya.
Magance wadannan batutuwan muhalli ya sami cikas ta hanyar rashin fahimta da sakaci a tsakanin al’ummomi. Koma dai yaya, hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki, kungiyoyi masu zaman kansu, da al’ummomin gida na iya yin amfani da karfin hadin gwiwa, kwarewa, da albarkatunsu don magance rikice-rikicen muhalli yadda ya kamata da habaka ci gaba mai dorewa.
A matakin farko, shirye-shiryen da al’umma ke jagoranta, suna karfafa al’ummomin yankunan da su jagoranci ayyukan muhalli, wanda kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomin gwamnati ke tallafawa.
A Jihar Zamfara, bisa kididdigar da aka fitar ya yi nuni da cewa, mutum 11,000 ne suka kamu ta hanyar shakar iska mai dauke da guba, yayin da 12,000 daga cikinsu ‘yan kasa da shekaru 6 ne.
An binciko kauyuka 47 inda a cikin kauyukan an samu mazauna yankin 30,000 da suka rasa matsugunansu saboda ayyukan hakar ma’adinai a yankin.
Manyan hanyoyin kamuwa da cutar su ne ta hanyar sha da shakar iska mai guba.
A sokoto kuwa, rashin samar da wurin zubar da shara, da rashin kula da sharar, gurbacewar muhalli da kuma toshe hanyoyin magudanar ruwa shi ya haifar da ambaliyar ruwa.
Alhassan Mansur a Jami’ar Jihar Sakkwato kuma mai bincike, ya gudanar da inda ya nuna cewa sharar gidaje ta kai kashi 53.5 na sharar gida a jihar da ake sarrafawa. Wannan ya tabbatar da cewa, rashin wayar da kan jama’a, da kuma samar da kayan aiki, shi ne babban dalilin rashin sarrafa shara.
A nan an ambaci kadan ne daga irin wannan mummunar illar da ke haifar da matsalar muhalli da kuma yadda suke shafar al’umma da daga gurbacewar muhalli a Kano, da sharar Katsina, da zaizayar kasa a Jigawa, da gubar dalma a Zamfara, da rashin sarrafa shara a Sakkwato, Hamada a Kebbi da ambaliya marar karewa a Kaduna.
Duk wadannan lamuran na nuni da yanayin lalatacewa da tasirin rayuwa na gurbacewar muhalli. Babban kalubalen warware wannan rikicewar shi ne wayar da kan jama’a yayin da Batun Jahilci ke ci gaba da ciwa mutane tuwo a kwarya a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya.
Kamar yadda ake karfafa wa mutane kan su je makaranta, bayar da bayanai yana da iya ga majiya mai tushe guda; kalmar da za ta bayyana daga baki. Rikicewar muhalli ya kasance babban batu mai mahimmanci wanda ke bukatar kowane hannu yayin warware matsalar. An fi magance wannan batu ta hanyar kafofin sadarwa.
Magance kalubale
Domin karfafa ikon kungiyoyin yada labaru, sashen UNESCO na Ci gaban Watsa Labarai cikin Gaggawa, inda a kwanan nan ya kaddamar da Canjin Yanayi a cikin shirin Watsa Labarai.
Dangane da yankuna da dama a duniya, ciki har da Nijeriya, wadanda ke fama da matsalar sauyin yanayi, UNESCO ta hada gwiwa da Cibiyar Binciken Jarida (CIJ) don horar da kungiyoyin yada labarai a Tsakiya da Yammacin Afirka.
Hukumar Kula da Babbar Ganuwa ta kasa (NAGGW) tana kokarin kare muhallan Nijeriya ta hanyar maido da alkinta filaye da inganta ayyuka masu dorewa. Suna wayar da kan jama’a, karfafawa al’umma, da samar da ayyukan yi ta hanyar sake dawo da su, wanda ke taimakawa tattalin arzikin cikin gida da rayuwa.
Gwamnatin Jihar Kano na dasa itatuwa miliyan 1.2 domin yaki da kwararowar hamada, kuma NAGGW tana horar da mata da su rika noman birket domin samar da makamashi mai dorewa da inganta lafiyarsu da rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli. Wannan kokari na nufin habaka juriya kan tasirin yanayi da kirkirar yanayi mai tsabta, mai samar da koshin lafiya.
Matsayin Kafofin Yada Labarai
A matsayinmu na ’yan jarida, yana da muhimmanci mu wayar da kan jama’a ta hanyar buga kasidu da aka yi bincike sosai, da rahotanni da sassan bincike.
Rahoton bincike ya yi fice a matsayin babbar hanyar ganowa, Ganewa da fallasa musabbabi, illolin da bayar da yiwuwar mafita ga rikicewar muhalli.
Haka nan za mu iya amfani da ba da labari a matsayin wata matsakaiciyar fasta don kara tausayawa da karfafa aiki.
Abubuwan ilimantarwa kamar ‘Infographic’, masu ba da bayani da tatsuniyoyi su ne manyan tushen Bayanai.
Sun ce tunanin kan hakan yana dadewa, don haka, za mu iya amfani da irin wannan hanyar wajen kirkirar hanyar wayar da kan jama’a. Aikin jarida na ba da shawara ta hanyar daidaita takamaiman dalilai na muhalli ko manufofi, inganta hanyoyin warwarewa da kuma rike ikon matakan da za mu iya dauka don ragewa da magance rikicewar muhalli.
Ba za a iya wuce gona da iri kan muhimmancin ‘yan jarida ba. Ta hanyar kokarinsu jarumtaka, da jajircewa, suna kawo mana muhimman bayanai daga ko’ina cikin duniya. Su ne a sahun gaba a cikin kokarin da muke yi don samun lafiya ta duniya da ingantacciyar rayuwa, suna ba da haske kan batutuwa masu mahimmanci da kuma daukar wadanda ke kan madafan iko.
Karshe
Duniya daya gare mu, gida daya da fili daya. Ba za mu samun damar kammala komai gaba daya ba, za mu iya kirkirar abin da muka zo dominsa. Muhallinmu muhimmin bangare ne na rayuwarmu.
Tsarin halittunmu, tsirrai, dabbobi da yanayinmu sun kasance wani bangare na mu. Ya zama alhakinmu don ragewa, habakawa da kuma dorewar wannan yanayi.
Mun shaida yadda wadannan rikicerikicen da ake fama da su a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya ke haifar da asarar rayuka, da raba iyalai, Gurbacewar abinci, tabarbarewar al’amura da kuma barna.
Ya zama wajibi a tura kayan aikinmu zuwa duniyarmu. Muna bukatar mu yi amfani da murya da kuma wayar da kan wasu game da kulawarta.
Yayin da al’amura ke ci gaba da haifar da tasiri marasa kyau ga jama’a da damuwa, yana da mahimmanci ga tashoshi irin wadannan kamar kafofin yada labarai su rika warwarewa, ragewa da kuma kawo karshensa.