Majalisar dattawa na shirin samar da dokar da za ta kafa hukumar tattara bayanai na ‘yan aikatau da kuma iyayen gidansu.
Majalsar ta ce za a samar da hukumar ne domin kare hakkin ‘yan aiki, wadanda ke fuskantar cin zarafi daga iyayen gidansu.
- Hajjin Bana: Nijeriya Ba Za Ta Yi Amfani Da Sararin Samaniyar Sudan Ba – NAHCON
- CBN Ya Bukaci Masu POS Su Yi Rajista Da Gwamnati
Kudirin dokar ya tsallake karatu na biyu ya nemi a kare iyayen gidan, wadanda a wasu lokutan ke fuskantar hatsari daga masu yi musu aikin.
“Idan kudirin nan ya zama doka to wajibi ne a bai wa ‘yan aikatau wajen kwana mai kyau kamar yadda mutum zai bai wa iyalinsa, ba za a ci mutuncinsu ba.
“Talauci ba zai zama hujjar da mutum zai mutuncin wani mutum ba,” in ji Sanata Babangida Hussaini.
Wannan dai na zuwa ne bayan kiranye-kiranye da kuma irin cin zarafin da ake yi wa ‘yan aikatau a Nijeriya.
A wasu lokuta masu aikatau na fuskantar hatsarin gaske, lamarin da ke kai ga salwantar rayukan wasu daga cikinsu.