A ranar 5 ga watan Mayun 2010 ne, marigayi tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar’Adua ya rasu, wanda a bana ya cika shekaru 14 da rasuwarsa.
An haifi Yar’Adua ne a ranar 26 na watan Agustan 1951, inda ya rasu yana da shekaru 59, wanda inda yana a raye har zuwa ranar ta 5 ga watan Mayu, da ya kasance yana da shekaru 73 a duniya.
- Da Ɗumi-ɗumi: EFCC Za Ta Gurfanar Da Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Da ‘Yarsa A Gobe Alhamis
- Majalisar Wakilai Ta Umarci CBN Ya Dakatar Da Harajin Tsaron Yanar Gizo
Ya rasu ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja, washe gari aka kai shi mahaifrsa ta Jihar Katsina aka yi masa zana’iza.
An ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 21 na watan Afirilun 2007, inda ya shafe shekaru uku a kan karagar mulkin kasar nan.
Kafin a zabe shi a mukamin shugaban kasa a inuwar jami’iyarsa ta PDP, an zabe shi a mukamin gwamnan Jihar Katsina daga 1999 zuwa 2007, inda kuma ya ci gaba gudanar da ayyukan da ya gada a gun gwamnatin baya ta jihar.
‘Yan’uwansa na kusa da abokansa na siyasa da wasu ‘yan Nijeriya na ci gaba da yin jimami dangane da rasuwar marigayin.
An ruwaito wasu daga cikinsu sun yi bayanai a kan irin salon shugabancinsa, inda suka bukaci sauran shugannin a kasar nan da su koyi da irin salon shugabancin marigayin nagari, mussamman domin a ciyar da Nijeriya gaba.
Wasu ‘yan Nijeriya da dama na kallon Yar’Adua a matsayin mutum mai kishin kasa wanda kuma ya hau karagar mulkin kasar bisa burin daidaiita harkar siyasa da bunkasa tattalin arzikin Nijeriya da inganta rayuwar ‘yan kasar.
Haka zalika, Yar’Adua ya kafa tarihi a ranar 28 na watan Yunin 2007, wanda shi ne shugaban kasa na farko da bayyana wa duniya kadarorinsa da ya mallaka.
Ya yi hakan ne a matsayin daya daga cikin cika alkwuransa na yakin neman zaben shugaban kasa domin ya zama misali ga sauran ‘yan siyasar a yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan.
Yar’Adua ya bayyana cewa ya mallaki kadarorin da kudinsu suka kai na naira 856,452,892 da kuma tsabar naira miliyan 19, wadanda mallakar mai dakinsanne Hajiya Turai Umaru ‘Yar’adua, sai kuma wasu kadarori da kudinsu suka kai na naira 88,793,269.77.
Bugu da kari, gwamnatinsa a watan Agustar 2007, ta kaddamar da shirin ajandodi bakwai don ta lalubo da mafita kan kalubalen da Nijeriya ke fuskanta a wacan lokacin.
Gwamnatinsa ta kuma kuduri aniyar dora kasar a jeren kasashe 20 da ke da karfin tattalin arziki a duniya kafin zuwan 2020.
Kudurrorin gwamnatinsa bakwai sun hada da, samar kayan aiki, wadatacciyar wutar lantaki, samar da wadataccen abinci, kirkiro da hanyoyin kudin shiga ga ‘yan Nijeriya, bunkasa fannin sufuri, samar da sauyi, inganta fannin tsaro da kuma bunkasa ilimi.
Haka zalika, marigayin ya mayar da hankali kan samar da sauyi a dokar zabe, inda har ya aminta da cewa hanyar da aka bi ya zama shugaban kasa cike take da kurakurai.
Wannan ne ya sanya ya kafa kwamitin kwamin da zai yi dubi a kan harkar siyasa da lamarin tsaro da suka janyo matsaloli ga ingancin gudanar da sahihin zabe a kasar a karkashin jagorancin tsohon Alkalin-alkalai na tarayya Mohammed Lawal Uwais.
Ya dai kikiro da shirin yin afuwa ga tsagerun Neja Delta.Wannan matakin na daya daga cikin manyan nasarorin da tsohuwar gwamnatin marigayin ta samu.
Tsohuwar gwamnatin Marigayi Yar’Adua, a ranar 25 na watan Yunin 2009, ta yafe wa tsagerun yankin Neja Delta da ke da hannu wajen aikata yi wa tattalin arzikin zagon kasa, wadanda suka nuna niyyar ajeye makamansu ta hanyar ba su wa’adin kwana 60. Wannan tsarin na daya daga cikin shawarwarin kwamtin sake farfado da yankin Neja Delta (NDTC).
Bugu da kari, wannan shirin na yin afuwa, ya haifar da kirkiro da ma’aikatar inganta rayuwar mazauna yankin Neja Delta a karkashin shirin fadar shugaban kasa na yafe wa tsagerun yankin (PAP).
A wancan lokacin, mazauna yankin da dama sun kasance sun cusa kansu wajen yi wa tattalin arzikin yankin zagon kasa da yin garkuwa da mutane domin kawai suma su amfana da dukiyar yankin mai albakatun man fetur.
Tsohuwar gwamnatin Marigayi Yar’Adua, ta mayar fa martani ta hanyar yin amfani da tsari mai tsawo, wanda ta umarci dakarun soji su kaddamar da kai farki mai karfi ta kasa da sama da kuma ta hanyar ruwa bisa nufin tarwatsa sansanan tsagerun yankin da suka ki ajiye makanansu, inda kuma ta yi wa sauran da suka ajeye makamansu afuwa ta kuma saka su a cikin shirin gwamnatin na inganta rayuwar mazauna yankin ta hanyar ba su horo a kan koyon sana’o’in hannu don su zama masu dogaro da kansu.
Wani karin gagarumar nasara da tsohuwar gwamnatin marigayin ta samu shi ne, rage farashin man fetur wanda hakan ya sanya dimbin al’ummar kasar suka yi wa tsowar gwamnatin mubayi’a.
A lokacin tsohuwar gwamnatin shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo da marigayin ya gada, a ranar 25 na watan Mayun 2007, kwana biyu kafin Obasanjo ya mika ragamar shugabancin kasar ga marigayin, ya kara farashin man daga naira 65 zuwa 75 kan kowacce lita daya.
Sai dai, marigayin bayan wata daya da ya dare karagar shugabancin kasar ya maido da farashin daga naira 75 zuwa naira 65 na kowacce lita daya.
Dimbin ‘yan Nijeriya sun yi maraba da wannan matakin na tsohuwar gwamnatin marigayin, musamman yadda matakin ya rage masu tsadar sufuri.
Haka kuma, wata babbar nasara da gwamnatin marigayin ta samu shi ne, soke tsarin tshowar gwamnatin Obasanjo na sayar da matatun mai biyu na kasar nan.
Tsohuwar gwamnatin Obasanjo, ta kammala kulla yarjejeniya da Aliko Dangote kan sayar masa da matatun man biyu, amma Yar’Adua ya dawo da matatun man ga kamfanin man fetur na kasa (NNPC).
Wannan matakin na Yar’Adua ya janyo rashin fahimta a tsakanin marigayin da ubangidansa na siyasa, Obasanjo.
Obasanjo ya kafa hujja kan cewar, Dangote ya kasance yana jagorantar masu zuba jari wadanda kuma suka zuba hannun jarinsu har dala miliyan 750 a matatin man fetur din biyu da gwamnatin tarayya ta wancan lokacin ta gaza kulawa da su.
Marigayin ya kuma dakatar da shirin da gwamnatocin baya da suka kirkiro da su na sayar da hannun jarin makarantu sakandare gwamnatin tarayya guda 102 da ke a daukacin fadin Nijeriya. Wadannan makarantu da aka fi sani da ‘Unity Schools’, an kafa su ne a 1970, bayan kammala yakin basasa a Nijeriya.
Manufar kikiro da su shi ne, don a hada kan yara manyan gobe na kasar nan da suka fito daga sauran sassan kasar domin su hadu a wadannan makarantun don samun ilimin zamani.
Amma, ita kuwa tsohuwar gwmanatin Obasanjo ta kirkiro da tsarin yin hadaka a tsanin gwamnati da mahukuntan makarantu masu zaman kansu da za su rinka kula da makarantun don samun riba, wanda ya bai wa gwamnatin damar kawo karshen tallafin da ake bai wa makarantun na gwamnatin tarayya.
Iyaye da kuma kungiyoyin malaman makarantun sun soki wancan yunkurin, inda suka bayyana cewa yunkurin zai fi karfin ‘ya’yan talaka na wajen samun ingantaccen ilimin zamani.
A 2007, Yar’Adua ya fuskanci ciwon koda, inda masu sukarsa suka fafata mahawara, domin a kawo karshen yama didin da suke yi a kan rashin lafiyarsa.
A ranar 6 na watan Maris din 2007, aka fitar da marigayin zuwa kasar Jamus bisa dalilai na lafiyarsa. Sannan daga baya aka kara fitar da shi a ranar 23 ga watan Nuwambar 2009, inda aka ruwaito cewa ana duba lafiyarsa a wani asibiti da ke kasar Saudiyya.
Daga nan nan ba a kara jin duriyar marigayin a wani taro a bainar jama’a ba, wanda hakan ya haifar da babban gibi a bangaren shugabancin kasar nan.
Kotun koli a ranar 22, na watan Janairun 2010, ta yanke hukuncin cewa majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta bayyana a cikin kwana 14, cewa Yar’Adua ba zai iya ci gaba da gudanar da ayyukansa a matsayin shugaban kasa ba.
Duk a cikin hukuncin kotun, ta umarci majalisar zartarwar ta saurari bayanai daga gun likitoci biyar da ke duba lafiyar marigayin.
Marigayi Yar’Adua, an dawo da shi a asirce zuwa Abuja a ranar 24 na watan Fabirairu 2010.
A wancan lokacin babu wani tabbaci dangane da yanayin rashin lafiyar margayin, sai dai an ta yin rade-radin cewa ana duba lafiyarsa a cikin motar daukar marasa lafiya, kafin daga bisani a sanya shi a cikin motar daukar marasa lafiya ta mussaman da ke a fadar shugaban kasa.
A wancen lokaci, an samu rashin fahimta da dogarin da ke tsaron lafiyar Yar’Adua, ya hana Goodluck Jonathan zuwa tarbar Yar’Adua.
A jawabinsa na mukaddashin shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya ce, tabbas rasuwar uban gidansa marigayi Yar’Adua babban rashi ne ga Nijeriya.