Gwamnatin Jihar Gombe, na shirin farfado da Masana’antun Auduga ta hanyar rugumar shirin gwamnatin tarayya na farfado da noman auduga, don bunkasa tattalin arzikin al’ummar jihar.
Gwamnan Jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya bayyana hakan, yayin da yake gana wa da tawagar ‘Kamfanin Arise Integrated Industrial Platform’ karkashin jagorancin Babban Mataimakin Shugaban Kamfanin Jacky Ribiere, a fadar gwamnatin jihar ta Gombe.
- Sabon Shirin Auren Zawarawan Kano A Sikeli
- Hajj 2024: NAHCON Ta Bukaci ‘Yan Jarida Su Yi Riko Da Gaskiya
Yahaya, wanda ya yi tsokaci a kan kokarin gwamnatin tarayya na sake farfado da noman auduga da masakun tufafi a Nijeriya, ya ba da tabbacin bayar da gagarumin goyon baya, domin saukaka farfado da noman na auduga a fadin jihar ta Gombe tare da yaba wa da kuma jaddada hangen nesan Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a kan hakan.
Ya kara da cewa, kasancewar Gombe jiha ce mai samar da auduga da wasu takwarorinta na Arewa kamar Katsina, Kaduna, da kuma Zamfara, akwai fatan sake farfado da noman auduga tare da sarrafa Irinta kamar yadda shirin farfado da noman audugan na gwamnatin ya kuduri aniyar yi.
Gwamna Inuwa, ya sake jaddada muhimmancin hada hannu da masu ruwa da tsaki; wadanda suka hada da Kungiyar Manoman Auduga ta Kasa (NACOTAN), don samar da cikakken tsarin farfado da noma da kuma sarrafa audugar.
Haka zalika, ya bayyana damammakin da ake da su na damawa da manoma a Karamar Hukumar Balanga da wasu sauran Kananan Hukumomin Kudancin Jihar, wadanda suke da matukar muhimmanci wajen noman wannan auduga a jihar.
“Sake farfado da sana’ar noman auduga, zai magance rashin aikin yi a tsakanin matasan Nijeriya tare da farfado da tattalin arzikin wannan kasa,” in ji Gwamnan. Sannan, ya bayyana Jihar Gombe a matsayin daya daga cikin jihohin da ake noman audugar, ya kuma yi alkawarin ci gaba da ba da kwarin guiwa ga noman na auduga, domin samun riba mai yawan gaske.
Bugu da kari, ya kuma shaida wa bakin nasa cewa, ganin yadda aka kafa sansanin masana’antu na Muhammadu Buhari, mai fadin hekta 1,000 a kusa da tashar wutar lantarki ta Dadinkowa; mai karfin megawat 40 da kamfanonin gurzan auduga da ake da su a Jihar Gombe, hakan zai tallafa wajen sake farfado da bangaren noman na auduga.
Har ila yau, taron ya samu halartar Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, da Kwamishinan Ciniki, Masana’antu da Yawon Bude Ido, Nasiru Mohammed Aliyu da kuma takwaransa na Ma’aikatar Noma da Kiwo, Dakta Barnabas Malle; kamar yadda Ismaila Uba Misilli, Babban Daraktan Yada Labarun Gwamnan Jihar na Gombe ya nakalto.