Turaren Kaya/Daki/Jiki
Ki sani uwargida ba wai sai maigida yana da wadata ne za ki yi tunanin neman ababen da za su gyara maki jiki ba domin kina tunanin duk wani abu na gyaran jiki tsada ne da shi, sai dai sirrin ina mai tabbatar miki ba haka bane, domin za ki iya gyaran jikinki cikin sauki da kudi kankani.
Sabulun salo za ki hada da sabulun Detol sai zuma yana gyara fata sosai, sai dai yana da mahimmanci ki san yanayin fatarki. In har mai saurin daukan zafi ce sabulun salo kar ya yi yawa, Sabulun Dobe Nebea, Garin Zaitun, Habbattu Sauda, Jar Dilka Kurkur, Sabulun Gana, Sabulun Dudu Osun, Lemun Tsami, Zuma mai kyau, Madaran Turare iri biyu mai matukar kamshi madara gari duk za ki goge sabulun sai ki hada su guri daya ki dama za su hade ki sanya su a firij ko guri mai sanyi.
 Busasshen zogale, Kori, Alo Bera, da Na’a na’a za ki hada su ki dan sanya man Zaitun amma ki tabbata kadanne za ki rinka shafawa fatarki za ta yi kyau da kyalli. Yawaita shan kayan itace masu sanya fata ta yi kyau da kyalli.
Cin nama da zuma ko nama da nono na gyara fata kuma yana taikamakawa maza wajen gyara jiki.
Hadin turaren Gaf-gaf Na Tsugonno
Abubuwan da za ki tanada:
Itacen gaf-gaf, Sukari, Jawul, Lemon Tsami, Misik, Farce, Hawi, Garin Sondol, Gallo, Madarar Turaren Zuzan, Madarar Turaren Sondol Rose, Madarar Turaren Binta Sudan, Madarar Turaren Sondol, Garin Sondol, Madarar Turaren Mena:
Za ki hada turaran gaba daya sai dai farcan bayan kin kuma daka shi za ki yi ya yi laushi, shi kuma itacen gaf-gaf din idan kika sayo za ki ganshi kamar kashi, sai kin jika kin wanke, sannan ki baza ya bushe, sannan ki farfasa a turmi, sai ki hada su waje daya ki dinga turara gabanki da shi ana turaren jiki ma da shi, amma kollon da hawi ma
Daka wa za ki yi ya yi gari ki zuba wani a gun soyawa.