Jama’a barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na TASKIRA, shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Ciki sun hadar da; zamantakewar aure, ratuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da wata wasika da shafin ya ci karo da ita, inda wasikar ta fara da cewa; “Malama yau na ga bakar safiya, ba fada ba komai mijina bayan ya yi sallar Asuba ya miko min takardar saki, kuma wallahi lafiya lau muke, jiya tare muka ci abincin dare muna ci muna hira, ina saka shi nishadi da walwala. Bayan na karanta takardar idona cike da kwalla na ce masa wane me na yi maka haka? sai ya ce min “zama ne ya kare kawai ki yi hakuri”, da ya ga kukana ya tsananta sai ya ce ‘ki yi hakuri ba son ki ne ba na yi ba, amman malamaina sun tabbatar min da cewa in har ina tare da ke ba zan taba yin arziki ba, sai dai na samu mai suna Safiyya na aura shi ne burujin sunanmu zai hadu’. Malama ya zan yi?, ni marainiya ce, yarana uku yanzu ma watana biyu da haihuwar ta ukun, babata da babana duk sun rasu na rasa yadda zan yi.”
Irin wannan matsalar tana nan tana addabar gidajen aure da yawa, wasu sun yi Imani da cewa idan har mutum ya auri mace mai farar kafa ba zai yi arziki ba. Wasu kuma su ce a’a, tauraruwarsu ce ba ta zo daya ba, alhali sun manta da cewa Allah ne mai azurtawa. Dalilin hakan ya sa shafin Taskira jin ta bakin mabiya shafin game da wannan batu; Ko me za a ce a kan hakan?, me ya ke janyo hakan?, wacce shawara za a bawa ma’aurata, musamman maza masu irin wannan dabi’ar?
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Jihar Kano, Rano:
Abin da zan ce a kan haka shi ne hauka da kuma rashin yarda da kowacce irin kaddara. Kwadayi da son abin duniya uwa uba hangen wasu wadanda suke da abin duniya wanda suke da shi ta halal da kuma wanda suka samu ta hanyar haram. Shawarata a nan ita ce masu irin wannan dabi’ar su daina, domin ba tada kyau, mu rika tuna cewa komai daga Allah ya ke balle kuma shi gashi Allah ya azurta shi da samun haihuwa har da yara guda 3, domin wallahi a kwai masu kudin da idan za su bayar da dukkan abin da suka mallaka su samu da ta hanya mai kyau za su yarda. Mu rika tuna cewa bawa ba zai mutu ba har sai ya gama samun duk wani arziki nasa, sannan sai ya cinye iya nasa sannan zai bar wannan duniya to maye abin biye zancen wasu ‘yan tsubbu?, Allah kasa mu dace amin.
Sunana Nabila Dikko, Daga Jihar Kebbi:
Maganar gaskiya zama da irin wadannan mazan ma akwai hadari, saboda watarana yaransa za a iya raba shi da su a kan neman duniya, abin da zan ce shi ne kiyi hakuri ki barwa Allah lamarinki, watakil ubangiji ya yi miki tanadi a gaba na samun miji nagari mai addini da imani, yaranki ki kula da su ki roka musu shiriya, ki samu ki nemi sana’a don ki dogara da kanki ubangiji ya dubi maraicinki. Son zuciya da kwadayin abin duniya su ke janyo hakan. Shawarata daya ce maza masu dabi’ar yawon neman arziki a wurin wanin Allah, to ku sani kun aikata shirka, ku ji tsoron Allah ku daina ubangiji shi ne mai azurtawa shi ne mai talautawa, babu wani mahaluki da zai baka arziki ba tare da amincewar Allah ba.
Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To da farko dai za a dauki abun a matsayin kaddara domin shi aure rai gare shi da kuma wa’adi babu yadda za a yi idan wa’adin rabuwa yayi dole ne sai an rabu babu makawa.To amma magana ta gaskiya indai babu wani laifi data yi masa to ya ci zarafinta, kuma zai yi wuya ya sake ta ba tare daya bayyana dalilin daya sa ya sake ta ba, domin duk da kaddara ce to dole a kwai sila da za ta zama tsanin sakin. To magana ta gaskiya ita da mijin nata su suka fi kowa sanin dalili domin zai yi wuya a ce babu wani dalili daya dogora da shi wajen aikata sakin, kuma zai yi wuya a ce bai bayyana mata ba ko kuma ya bayyanawa wakilinta, don haka ba za mu yi gaggawar yanke hukunci ko goyon baya ba, domin ba mu ji daga bangaren mijin ba, don haka addu’a za mu yi Allah ya daidaita tsakaninsu. To magana ta gaskiya ya kamata mutum duk abun da zai yi ya ke tunani, kuma ya sani shi ma wata rana uba ne kuma siriki don haka bai kamata ba ka yiy wa ‘yar wani abun da idan a ka yi wa ‘yarka ba za ka ji dadi ba, domin wani abu da ka yi wa ‘yar wani da zummar cin mutunci ko cin zarafi tofa wata rana kai ma sai an yi wa ‘yarka, daga karshe nake kira ga mazaje da ma matan da ya kamata mu ji tsoron Allah mu dauki aure a matsayin ibada mai girma kuma mai muhimmanci, kuma a nemi ilimi kafin ayi auren domin zai taimaka wajen rike auren da daraja sosai.
Sunana Hadiza Muhammad, Daga Gusau Jihar Zamfara:
Hakika wannan lamari ya kazanta, abun da zan ce a kan hakan shi ne; gaskiya wannan ba abokin zama bane. Ba abun da zai janyo haka face jahilci, da kuma san zuciya. Shawara daya ce su ji tsoron Allah, su kuma tsarkake zuciyarsu. Su sani ba mai azurtawa ba kuma mai talautawa face Allah, Allah ya sa mu dace.
Sunana Abubakar Usman Malam Madori, A Jihar Jigawa:
Sai dai mu ce Allah ya kiyaye gaba domin mai faruwa ta riga ta faru. A mafi yawancin lokaci rashin tauhidi da rashin ilimi na zamani da kuma rashin waye wa shi ke kawo irin wannan sabanin a tsakanin ma’anauta, da kuma hangen na sama da kai, duk wanda ba zai kalli na kasansa ba, sai dai na samansa to zai rayu cikin kaskaci da rashin wadatuwa da abun da Allah ya ba shi. Ka zamto mai tauhidi wannan zai sa, ka rayu cikin aminci. Ana so duk musulmin kwarai ya dauka cewa an fi shi, shi ma ya fi wani, idan ka dauka wa kanka wannan mataki to za ka samu nutsuwa a cikin rayuwar ka tare da iyalinka. idan a ka samu akasin haka to irin wannan ce za ta rika faruwa, Allah ya kyauta. Wacce shawara za a bawa ma’aurata musamman maza masu irin wannan dabi’ar?. Shawarata ta farko a nan ita ce; ‘yan’uwana maza su gamsu cewa Allah shi ne ya ke azurtawa shi ya ke talautawa, idan duk duniya za su taru su ce za su azurtaka idan Allah bai nufe ka da arziki ba wallahi basu isa ba, haka kuma idan Allah ya azurta ka, idan duniyar za su taru dan ganin sun talautaka wallahil’azim basu isa ba, saboda haka ina kira ga mazaje da su dinga sanyawa zuciyarsu tawakalli da hangen nesa da kuma neman na kai ta hanyar halal, domin kaucewa rayuwar bogi, da kuma sanyawa a rai na fi wani ni ma an fi ni, Allah ya sa mu da ce.
Sunana Fatima Tanimu Ingawa daga Jihar Katsina:
Wannan shi ne babban tashin hankali wanda ba a sa mashi rana, a gaskiya tushen matsaltsalun kawo tsaiko na zaman lafiya bai wuce nasaba da tasirin bokaye ba a cikin al’umma. Su ke hada fitintinu kama daga gidagen wasu ma’auratan, ‘yan-kasuwa, ‘yan-siyasa da dai sauransu. Babban abun da ke jaho hakan a zamantakewa shi ne rashin ilimin addini har ma dana zamanin, wannan ke janyowa suke zuwa gurin bokaye masu ado da sunan malunta, suna kuma kawo masu kalubale sosai da sunan “ilimin-taurari” wanda hakan ke kaiwa ga mace-macen aure ko kuma wani kalubalen ga ma’aurata. Shawara shi ne ya kamata ma’aurata su ci gaba da neman ilimin addini ba gajiyawa, haka zalika mazan da abun ya fi shafa su dage da neman ilimin addini matuka don kauce wa da-na-sani da kuma samun dama tsantsar dayanta Allah ba tare da fadawa ga halaka ba. Allah ya sa su gane su gyara.
Sunana Hafsat Sa’eed, Daga Jihar Neja
To ni dai a tawa fahimtar babu tauhidi a wannan maganar ta shi da ya yi mata babu wata mace, in Allah ya tashi jarabtarka zai jarabce ka. Abin da ya ke janwo hakan wasu ziga ne, wasu kuma malamai ‘yan tsbbu ke gaya musu su kuma su yarda saboda rashin tauhidi. Shawarata ga ma’aurata a yi hakuri a yarda da kaddara me kyau ko akasin hakan, Allah ya sa mu dace.