A yau Litinin ne hukumar kwallon kafa ta Nijeriya za ta kaddamar da Finidi George a matsayin babban kocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya.
Daraktan Sadarwa na NFF, Ademola Olajire, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Lahadi a Abuja, inda ya ce taron zai samu halartar ministan wasanni, Sen. John Owan Enoh da babbar sakatariya a ma’aikatar, Mrs Tinuke Watti da shugaban NFF, Ibrahim Gusau da babban sakataren NFF, Mohammed Sanusi, da sauran manyan mutane.
- Finidi George Ya Zama Sabon Kocin Super EaglesÂ
- Kocin Super Eagles Jose Peseiro Ya Ajiye Aikinsa Bayan Karewar Kwantiraginsa
Finidi George ya ajiye aikin horar da kungiyar Enyimba Fc da ke Aba kwanakin baya, inda Enyimba FC take matsayi na uku a gasar NPFL, da maki 53 a wasanni 32 da tazarar maki hudu tsakaninta da Enugu Rangers da ke kan teburi, sai kuma Remo Stars da take a matsayi na biyu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa George mai shekaru 52 ya shafe watanni 20 a matsayin mataimaki ga tsohon kocin Super Eagles José Peseiro.