Kocin tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta Nijeriya, Jose Peseiro, ya bayyana aniyar ajiye aikin horar da tawagar bayan karewar kwantiraginsa.
Peseiro, ya shafe watanni 22 yana jagorancin tawagar, inda suka kai wasan karshe na gasar cin kofin Nahiyar Afirika da aka kammala a kasar Cote de ‘Voire.
- Kasar Sin Na Kokarin Samar Da Hidimomin Biyan Kudi Masu Sauki Ga Baki
- ‘Haɗewar NILEST Da NARICT Barazana Ce Ga Walwala Da Ayyukan Cibiyoyin’
Duk da cewar hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF) na duba yiwuwar tsawaita kwantiragin nasa.
Talla
Peseiro ya bayyana wannan aniyar a shafinsa na X, inda ya gode wa hukumar a kan yadda ta ba shi goyon baya a tsawon lokacin da ya kwashe a Nijeriya.
Talla