Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya ce Sin za ta ci gaba da fadada bude kofa, da raba ribar ci gaban ta da sauran sassan duniya. Han ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin jawabin bikin bude taron kasa da kasa na yayata harkokin cinikayya da zuba jari na shekarar 2024, wanda ya gudana a birnin Beijing.
A cewar sa, ta hanyar bunkasa harkokin kasuwanci, da ‘yantar da hada hadar zuba jari, da tabbatar da juriya da daidaiton tsarin samar da hajoji na sassan duniya, da gudanar ayyukan masana’antu bai daya ne za a iya wanzar dankon hadin gwiwa, da fadada cin gajiya tare.
Daga nan sai Han Zheng ya yi kira da a kara azamar amfani da damar da ake da ita, ta sabbin zagayen sauye sauyen fasahohi da masana’antu, da karfafa kirkire kirkiren kimiyya da fasaha, da bunkasa sabbin matakan samar da ci gaba. (Saminu Alhassan)