An kama wasu ‘yan kungiyar ta’adda na Boko Haram suna amfani da na’urar Starlink, na’urar da ke da hanzari sosai wajen sadarwa ta yanar gizo, na’urar mallakin hamshakin attajirin nan Elon Musk ce, suna amfaninda na’urar a dajin Sambisa.
A cewar wani kwararre mai bincike kan harkokin ‘yan ta’adda, Zagazola Makama, ya ce, Sojojin Nijeriya da ake kira “Operation Hadin Kai” sun yi nasarar kashe wani babban kwamandan kungiyar, Tahir Baga, tare da gano hanyoyin da yake amfani da su wajen sadarwa ta amfanin da Wi-Fi na Starlink da wayoyin hannu na zamani da dai sauransu.
- Tubabben Kwamandan Boko Haram Ya Bayyana Ta’asar Da Suka Tafka A Sambisa
- Wani Shahararren Dan Boko Haram Ya Mika Wuya Ga Sojoji A Borno
Kamfanin Starlink wanda mallakin attajiri ne na biyu a duniya, ya sanar da kasancewarsa a Nijeriya a watan Janairun shekarar 2023 da nufin samar da hanayar sadarwa ta intanet mai rahusa zuwa wuri mai nisa a kasarnan kuma ana sayar da shi kan Naira 450,000.
‘Yan ta’addar dai sun ranta a na kare tare da barin kayayyakinsu a lokacin da suka gaza jurewa musayar wuta daga dakarun sojojin Nijeriya.