Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kaduna ta ce, a ranar 23 ga watan Mayun 2024, za a fara jigilar maniyyatan jihar zuwa kasa mai tsarki (Saudiyya).
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Yunusa Muhammad Abdullahi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
- Kotu Ta Daure Wani Mutum Wata 2 A Gidan Yari Kan Satar Doya
- Sanata Hanga Ya Kare Sukar Da Ake Yi Masa Kan Tallafin Tukwanen Yumɓu Da Likafani
Sanarwar ta ce, an ware wannan ranar ce, bayan tattaunawa da hukumar jihar ta yi da hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON da kuma wasu wakilan kamfanin jiragen sama na Max Air wanda aka amincewa jigilar maniyyatan jihar zuwa Saudiyya.
Sanarwar ta kara da cewa, jimillar maniyyatan jihar 4,776 ne suka kammala biyan kudinsu na aikin hajjin bana.