Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa, gwamnati da hukumomin tsaro a kasar nan sun gaza wajen samar wa da ‘yan Nijeriya tsaron da ya dace.
Jihar Katsina dai na daya daga cikin jihohin kasar nan da ayyukan ‘yan bindiga ya yi kamari matuka.
- Kasar Sin Za Ta Tsaya Kan Manufar Bude Kofarta Ga Duniya
- Masu Gidajen Burodi Na Shirin Tsunduma Yajin Aiki
Da yake mayar da martani kan kalubalen na rashin tsaro da Nijeriya ke ci gaba da fuskanta, musamman a yankin Arewa Maso Yamma, Masari ya ce “Mutane sun dogara ne a kan jami’an tsaro da gwamnati wajen kare rayukansu amma kuma duk mun gaza.”
Masari wanda ya sanar da hakan a hirarsa da sashen BBC Hausa, ya ce, idan aka dubi lamarin har jami’an tsaro da dama sun rasa rayukansu .
Ya ci gaba da cewa, “Ba Katsina ce kadai ke fuskantar kalubaken rashin tsaro ba, matsala ce da kusan ta shafi jihohin kasar nan har da kasar Nijar da ke makwabtaka da mu.”
Ko da yake Masari ya ce, “An samu ci gaba wajen rage matsalar sabanin a baya, amma har yanzu ba mu iya kai wa ga karshen kalubalen na rashin tsaro ba.
Masari ya kuma yi fatan cewa Nijeriya za ta fice daga cikin matslar ta rashin tsaro, musamman a jihar Katsina kafin gwamnatinsa ta mika mulki ga wata gwamnatin da za ta zo a nan gaba.