Jami’ar Tarayya da ke Birnin Kebbi, FUBK ta gudanar da bikin daukar dalibai 2,217 da za su yi karatun digiri na farko da na biyu a Fanni daban-daban, a harabar jami’ar da ke Unguwar jaji a karamar hukumar Kalgo a Jihar.
An kafa jami’ar ne a cikin shekarar 2013 kuma ta fara karatu tare da dalibai a cikin shekarar 2014 inda take da sashin digiri 24, ya zuwa yanzu tana da sashin karatun digiri 37 da sashin karatun gaba da digiri na farko guda 20.
- Da Ɗumi-ɗumi: Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Jihar Legas, Soyannwo Ya Rasu Yana Da Shekara 55
- Emefiele Ya Ki Amincewa Da Tuhumar Da Ake Masa A Kotu
A nasa jawabin, Shugaban jami’ar Farfesa Zayyan Muhammad Umar ya bayyana cewa, jami’ar a shirye take ta yi amfani da kudadenta tare da karfafa ribar da take samu a halin yanzu domin bude sabbin hanyoyin samun dama ga ma’aikatanta da dalibanta.
Wannan bikin taron daukar Dalibai da jami’ar ta yi dai, shi ne karo na 9 tun bayan kaddamar da Jami’ar a shekarar 2013.
“Jami’ar ta karbi bukatar dalibai 2,530 da suka nemi gurabun karatun digiri na farko a jami’ar a wannan zango, an bai wa dalibai 2,269 damar yin rajista amma 2,095 ne kadai suka yi nasarar samun gurbin karatu.
“A matakin digiri na biyu, an samu jimillar Dalibai 112 da suka nema, kuma duk suna ci gaba da karatunsu a halin yanzu.” inji shi.