Mai martaba Sarkin Yauri, a jihar Kebbi, Dr Muhammad Zayyanu-Abdullahi, ya roƙi gwamnatin jihar da masu hannu da shuni da su cigaba da ƙoƙari wajen samar wa da matasan yankinsa aikin yi.
Sarki Zayyanu-Abdullahi, wanda shi ne Sarkin Masarautar Yauri na 42, ya yi wannan roko ne a garin Yauri a yayin bikin cikarsa shekaru 25 akan karagar mulki a ƙarshen mako.
- …Nijeriya Na Asarar Naira Biliyan 4.8 Duk Shekara Kan Rikicin Manoma Da Makiyaya -Mercy Corps
- Yadda Ƙungiyar Matasan Arewa Kan Harkokin Tsaro Ta Shirya Tattaunawa Kan Batun ‘Yansandan Jihohi
Sarkin ya ce,”Ina kira gare ku da ku ci gaba da ƙara samar da guraben ayyukan yi ga matasan mu masu domin maganin masu amfani da rashin aikin yi don hana su tada zaune tsaye domin rashin zaman banza shi ne uwar dukkan munanan dabi’u.”
Mai martaban ya yi nuni da cewa, hadin kan masu ruwa da tsaki ba wai kawai zai kawo ayyukan ci gaba a yankin ba ne, har ma da samar da yanayi na samar da ababen more rayuwa da dama.
Ya kuma bukaci manoma da su dasa duk wani nau’in amfanin gona da ake da su a yankinsa domin a samu saurin bunƙasar noma, “sarautar al’umma ta noma ce don haka dole ne su nuna wa duniya cewa za su iya ciyar da al’umma.
“Mu manoma ne a masarautar Yauri, muna da komai a yalwace, za mu iya noma albarkatu da yawa a Masarautar mu.
Sarki Zayyanu-Abdullahi ya godewa mutanen Yauri bisa goyon bayan da suka ba shi tun daga hawansa karagar mulki.
“Kuna ba ni goyon baya a ƙoƙarina na kawo ayyukan raya ƙasa da ci gaba a Masarautar mu.
“Don haka ina yi muku wasiyya da shuka waɗannan amfanin gona domin ci gaban masarautar Yauri,” A cewar mai martaban.
Daga ƙarshe, Sarkin ya godewa Gwamna Nasir Idris da jami’an gwamnatin jihar da sarakunan gargajiya bisa goyon bayan da suka ba masarautar domin samun nasarar cika shekaru 25 akan karagar mulki.