Babbar Kotun Tarayya da ke da zamanta a Abuja, karkashin jagorancin mai shari’a Alkali Emeka Nwite, ta karbi Dala 61,400 a matsayin sheda da aka danganta su da DCP Abba Kyari, kan zargin bai wa NDLEA.
Mai shari’a Emeka, ya karbi shaidar ne bayan da Peter Joshua, dan sanda mai gabatar da kara na uku ya gabatar wa da kotun shaidar.
- ‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Shugaban Jam’iyyar APC A Edo
- Darajar Naira Ta Sake Faduwa Warwas A Kan Dalar Amurka
Wadanda kotun ke tuhuma su ne, Sunday Ubua, ASP Bawa James, Insfekta Simon Agirigba da kuma Insfekta John Nuhu, yayin da kuma ake ci gaba da farautar ASP John Umoru.
A zaman kotun a jiya Laraba, jami’in NDLEA, Joshua ya shaida wa kotun cewa, an ba shi Dala 61,400 ne a ranar 25 ga watan Janairu bayan an gudanar da karamin bincike a kan kudin.
NDLEA dai, ta yi ikirarin ta samo faifan bidiyon da ke dauke da Abba Kyari na karbar Dala 61,400 a matsayin cin hanci daga wurin wasu jami’anta masu yin bincike don ta gabatar da hujja kan zargin badakalar hodar iblis kilo 17.55.
Wannan na daya daga cikin zargin shigo kilo 21.35 na hodar Ibilis cikin kasar nan da aka yi ta filin jirgin sama na Akanu Ibiam da ke a Jihar Enugu daga ranar 19 zuwa ranar 25 ga watan Janairu.
Shaidar ya kuma gabatar wa da kotun kwali 24 na hodar Ibilis da ke dauke a cikin wasu jakunkuna biyu, inda kotun ta dage sauraren karar zuwa ranar 30 ga watan Agusta 2022.